Assalamu alaikum
ILLOLIN ZAMA DA MACE DAYA (1)
HADARIN ZAMA DA MACE DAYA!!!
Mal Aminu Daurawa kano.
Zama da mace daya yana kawo illoli da dama ga
magidanci da su mata kansu da kuma
al`umma.
++++++++++++++++++
ILLOLI GA MAGIDANCI.
1:-Yana rage masa nishadin aure.
2:-Yana kawo tsufa da wuri.
3:-Yana saka maigida cikin damuwa
4:-Yana saka wa mace ta rika daga masa kai,
tayi masa yadda taso saboda ta san ba shi da
yadda zai yi.
5:-Yana rage masa samun soyayya da tarairaya
da kulawa da ya cancanta a matsayinsa na
maigida.
6:-Yakan hana shi tantance so na gaskiya daga
bangaren matarsa ko wanin haka.
****
ILLOLI GA SU MATAN.
1:-Yana hana wadansu samun mazajen aure.
2:-Yana dorawa matar gida aiyukan da suka
shige misali kamar, kulawa da maigida, yaran
gida da ita ma kanta.
3:-Yakan hana mace samun isasshen hutu da
kuma lokacin kulawa da kanta.
4:-Yana rage wa mace kuzarin nuna soyayya ga
maigidanta.
5:-Yana saka matar gida cikin tsoro da fargaba
maras yankewa na ko za ai mata kishiya.
6:-Yana haifar da rashin amincewarta ga
maigidanta da dauwamar da tuhuma ta har
abada.
7:-Yana saka mace cikin shirin yaki da
dawainiyar dakon makamai marasa ranar
yankewa na nuna kin ayi mata kishiya.
8:-Yana saka mata yawan zargi ga dukkan matan
da suke da alaka da maigidanta ko ma wace iri
ce koda ma yar uwa ce ko abokiyar
kasuwancinsa.
9:-Yana kara mata zafin kishi da rashin nutsuwa
marasa ranar yankewa.
****
ILLOLIN GA AL`UMMA
1:-Yana haifar da karuwai mata marasa aure.
2:-Yana bunkasa yawan zawarawa acikin
al`umma.
3:-Yana dorawa al`umma karin nauyin kulawa da
mata iyayen marayu da marayun kansu.
4:-Yana bunkasa zinace-zinace a cikin
al`umma.
5:-Yana rage tausayi da son bada taimako da
agaji daga zukatan al`umma.
6:-Yana kara saka fargaba da tsoro a zukatan
iyaye wadanda suke da `ya`ya mata a gaba.
7:-Yana bunkasa kasuwar malaman tsibbu da
bokaye.
Kuci gaba da kasancewa damu akoda yaushe
0 Comments