MAGANIN CIWON SANYI NA MATA

MAGANIN CIWON SANYI NA MATA
**************************************
Hakika ciwon sanyi na mata yana daga cikin
cututtuka masu wuyar magani, kuma mata da
yawa suna shan fama dashi.
Ga wata fa'idah nan daga ZAUREN FIQHU ku
jarraba, In sha Allahu za'a samu waraka.
Anemi :
1. Garin Tafarnuwa.
2. Saiwar Raihan (Doddoya - Rai dore)
3. Garin Kanumfari da citta.
4. Saiwar Zogale.
Wadannan abubuwan gaba daya ahadasu
adakesu waje guda, sannan arika diban
cokali guda ana dafawa ana sha kullum safe
da yamma.
Sannan adebi wani ahada da barkono ayi
yaaji dashi arika cin abinci. In sha Allahu
koda sanyi yayi shekara arba'in ajikinki ko
fiye da haka, zaki warke.
Hakanan Mazaje masu fama da matsalar
Sanyin mazakuta, Idan sukayi wannan hadin
zasu samu waraka da izinin Allah (SWT).
Tukwicin da za'a bani shine ayi Salati guda
goma bisa Masoyina, Shugabana, abin
koyina, Muhammadur Rasulullahi (Sallal
Laahu alaihi wa aalihi wa sallam).

Post a Comment

0 Comments