Hausa Novels: FANSAR FATALWA Page 1



 *FANSAR FATALWA* 
       ( _Horror Story_ 💀☠️). 
  _Tsarawa / Rubutawa_ 
 © *SHAMSIYYA MANGA* 
 *MANAZARTA WRITER'S* *ASSOCIATION* 
 *SADAUKARWA* _Wannan book É—in gaba É—ayan shi Sadaukarwa ne gareku Anty Hadiza D_ _Auta_Anty Binta Umar Abale, _sis Amira Adam_ _Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda kuke ina son ku fisabillillahi._ 
      *NOTE* 
Wannan labarin haƙƙin mallakata ne ban yadda a juyamun labari ta kowace fuska ba yin hakan babban kuskure ne.Sannan Labarinnan ƙirƙirarran labari ne ban yi shi dan cin zarafin wani ko wata ba kamanceceniyar labari akasine.
       *Free book*
-------------------------------------
 *Bissimillahir rahmani rahim* 
        *001* 
_________________________
 *ƘAWAYE* ! Hmmm idan naji wannan kalmar a kullum sai naji zuciyata kamar zata tarwatse saboda yadda na tsani jin an ambaci kalma mai kama da Ƙawance,tabbas Ƙawaye sun min babbar illa a rayuwata,tabbas Ƙawaye sun zama wani sashe daga cikin sashin tarwatsewar farin cikina,tabbas Ƙawaye sun illata rayuwa ta illa mafi muni. A wasu lokutan Ƙawaye su kan zama alkhairi ga rayuwarmu while a wasu lokutan kuma su kan zama babban sharrin da yake tarwatsa duk wani farin ciki na daga cikin rayuwar tamu kamar yadda ya faru a kaina. A zamanin baya Ƙawaye tabbas su kan zama alkhairi a rayuwar mu amma banda wannan zamanin da muke ciki in da kaso tamanin daga cikin kaso É—ari na Ƙawaye suke ba abun yadda ba,da yawa daga cikin Æ™awaye suna zaune da juna ne ba da zuciya É—aya ba sakamakon hassada da ta yiwa zukatan su katutu.Na tsani Ƙawance! na tsani duk wata kalma mai alaÆ™a da Ƙawance,na kasance mai wata iriyar zuciya wadda nake saurin yadda da mutane musamman Ƙawaye ina matuÆ™ar basu muhimmanci kafin su min Illah,idan zan zauna da mutum to ina bashi duk wata yarda da ta dangance ni sannan akan Ƙawa na gwammaci a cimun mutunci akan a ciwa Ƙawata,duk bayanin da zan muku ba zaku taÉ“a gane irin yadda na yadda da Ƙawance ba,sai dai ashe bansan cewa hakan babban kuskure bane nake aikatawa Sai da suka mun Illa kafin na farga. Ƙawaye sun illata rayuwa ta illa mafi muni inda suka yi nasarar tarwatsa duk wani jin daÉ—i da farin cikin da na mallaka ba kuma komai ne ya janyo hakan ba sai tsantsar hassada da kuma son zuciya.
****
Gudu take tsalawa a kan titin wanda zamu iya Æ™iran shi da gudun ceton rai duba da yadda take gudun ko kallon inda take jefa Æ™afarta ba tayi, dare ne sosai Æ™arfe biyu da rabi, bakajin motsin komai face kukan Æ™waruna da baza'a rasa ba,Tsananin duhun daren ya sanya ko tafin hannun ka baka iya gani,ga wata irin tsawa da ake yi mai firgitar wa wadda hakan yake nuni da cewar akwai hadiri sosai a garin wanda a kowane lokaci ruwa zai iya É“arkewa. Juyawa tayi ta kalli bayanta don ganin shin ko ta tsaracewa abun da take gudu É—in,sai dai kash! Da ta san abun da zata yi tozali da shi da bata juya ba domin kuwa tana juyawa tayi arba da abun da take gujewa É—in daf da ita,wani irin ihu ta sake tana fatan ko Allah zai sa wani ya jita domin a kawo mata É—auki duk kuwa da cewa ba lalle ko an jita É—in a fito ba,sai dai abun da bata sani ba shine duk ihun da take É—in babu mai jin ta. Bata ankara ba sai ji tayi taci karo da wani Æ™aton dutse da yake gefen titin  sai gata warwass a Æ™asa take ta fara gangarawa zuwa gefen titin inda yake wani wawakeken rami ne a wajen,daf da ta kusa faÉ—awa cikin ramin taji an ruÆ™ota buÉ—e idanunta ta fara yi a hankali tana jin zuciyarta tana mata wani irin bugu,  Tarwal ta buÉ—e idon nata  take tayi arba da abun da take gujewa É—in wanda hakan ya sanya ta É—aukewar jin ta da ganin ta sakamakon tsoratar da tayi É—in. Zazzafan ruwan da taji ya sauÆ™a a jikin ta ne ya bata damar farfaÉ—o wa daga sumar da tayi É—in,wani marayan kuka ta sake inda ta fara magana cikin wahaltacciyar murya.
"AMRAH dan Allah ki yi haƙuri ki taimake ni kar ki kasheni, wallahi nayi dana sanin duk abun da muka aikata miki dan Allah ki duba girman Allah ki yi haƙuri".
Wata dariya AMRAH ta sake wadda ni kaina sai da kunnuwana suka É—auke ji na wani lokaci,take kuma ta fashe da wani irin kuka mai ban tsoro a lokaci guda kukan suka shiga fitowa tare da dariya, haÉ—e fuska tayi kamar ba ita tayi dariyar ba sannan ta fara magana cikin muryar ta mai tsoratar wa.
"Ashe kinsan girman Allah!?, Afrah nace ashe kinsan Allah!?,Hmmm wai shin ko kin manta irin tozarta mun rayuwa da ku kayi?,shin kin manta jefamun rayuwa da ku ka yi a cikin tashin hankali da masifa?,ki sani idan maye yaci ya manta to uwar É—a ba zata taÉ“a mantawa ba.Sannan  ki sani wallahi nayi alÆ™awarin yadda kuka rabani da farin ciki a rayuwata to tabbas kuma sai kun É—anÉ—ani baÆ™in cikin dana É—anÉ—ana,ai matuÆ™ar ban dawo ÆŠAUKAR FANSA ba to bazan taÉ“a yafewa kaina ba, domin kuwa rama cuta ga macuci ibada ne,dan haka ki shirya girbar abun da kika shuka".
AMRAH tana kaiwa nan a zancen ta ta saki wata mahaukaciyar dariya wadda ta sanya wa tsuntsaye saurin tashi daga kan bishiyoyin da su ke tsabar tsorata,ita kuwa Afrah take wannan dariyar ta sanya mata É—aukewar jin ta da ganin ta na wani lokaci, AMRAH ce ta sanya dogon hannunta mai cike da dogayen farata ta cakawa Afrah a tsakiyar Æ™wayar idonta,wani gigittaccen ihu Afrah ta sake sannan ta tafi luuuu zata faÉ—a cikin wannan ramin,harshenta AMRAH  ta sanya wanda ya kusa kaiwa tsayin wani mutum É—in sannan ta nannaÉ—e Afrah  dashi ta jata ta nufi wani Daji da yake gefen titin da ita.
*****
Yau gidansu Afrah tun ƙarfe shida da suka farka basu koma ba sakamakon shirin auren Afrah ɗin da suke ta yi wanda za'a ɗaura nan da kwana uku in sh Allah shiri sosai akeyi a gidan kowa ka kalla fuskar shi cike take da farin ciki.
Wata farar mata ce doguwa ta fito daga cikin wani ɗaki ta sha ƙunshi na jan lalle abun ka da farar fata sai ya mata kyau sosai,kallo ɗaya zaka mata ka fahimci cewa mahaifiyar Afrah duba da yadda suke mugun kamanni, kallon ƴanmata da suke zaune a kan kujerar falon tayi suna shirya kaya a cikin wani akwati,wanda sun kai su goma sannan tace.
"Fadila wai nikam ina Afrah take ne har yanzu bata fito ba gashi har mai mata lalle ta ƙaraso?".Ta faɗa tana mai kai duban ta ga ɗaya daga cikin ƴanmatan.
"Hmmm Mom kinsan halin ƴar gidan naki bata son kwana a cikin mutane wallahi tana ɗakin baƙi jiya a can ta kwana ita ɗaya" ɗaya daga cikin ƴan matan ta faɗa tana mai cigaba da sanya kayan a cikin akwatin.
"Ke Husnah je ki taso ta dan Allah ta haƙura da wannan baccin asarar da take ɗin ita da bacci baya isar ta" cewar Mom ɗin tana juyawa dan komawa cikin ɗakinta.
Tashi Husnah tayi ta nufi hanyar ɗakin baƙin domin dubowa Afrah ɗin,turus! taja ta tsaya lokacin da ta shiga cikin ɗakin ganin ba kowa a cikin ɗakin,bakin toilet ta ƙarasa tana ƙiran sunan Afrah amma shiru ba alamar za'a amsa mata.
Da sauri ta kama handle ɗin jikin ƙofar toilet ɗin sannan ta tura ƙofar to her surprise sai gashi ƙofar ta buɗe shiga tayi cikin toilet ɗin inda ta fara ƙarewa kowace kusurwa da take cikin toilet ɗin kallo sai dai babu Afrah babu alamar ta, juyawa tayi ta fito daga cikin toilet ɗin cikin sauri ta nufi hanyar komawa cikin falon dan sanarwa da Mom abun da yake faruwa ɗin,tun daga bakin ƙofar ɗakin baƙin ta shiga ƙwalawa Mom ƙira cikin ruɗewa.
"Kai Husnah wai lafiyarki kuwa kike mun wannan ƙiran haka kamar zaki tashi sama,ina Afrah ɗin?" Mom ta faɗa wadda take fitowa daga cikin ɗakin nata.
"Mom ina kuwa lafiya Afrah fa bata cikin ɗakin baƙin".Husnah ta faɗa tana mayar da numfashi kamar wadda tayi gudu.
"Bangane ba wace irin magana kike haka wai Afrah bata ɗakinta?" Mom ta faɗa tana nufar hanyar ɗakin baƙin.
Juyawa itama Husnah tayi tabi bayan Mom ɗin inda suma su Farida suka miƙe gabaɗaya tare da rufawa Mom ɗin baya.
Duk wani bincike da su Mom zasu yi a cikin ɗakin sun yi shi amma babu Afrah babu alamarta,tun abun bai fara ɗaga musu hankali ba har takai sun fara tsorata da lamarin domin kuwa tun suna bincike iya cikin ɗakin har takai sun fito sauran sashin cikin gidan amma ko mai kama da Afrah basu gani ba,sosai hankalin su ya tashi inda suka koma cikin gidan Mom ta ɗauki wayarta ta ƙira Dad ɗin Afrah domin shaida mishi halin da ake ciki kasancewar tun da yayi sallar asubah bai shigo cikin gidan ba suna massallacin ƙofar gidan tare da mutane.
Yana ɗaga wayar Mom ta fashe da kuka tana sanar mishi ganin Afrah ɗin da ba'a yi ba,shima sosai hankalin shi ya tashi inda ya nufo gidan cikin sauri tare da yayun Afrah ɗin.A tsaye suka tarar da mutanen gidan cirko-cirko a harabar gidan tashin hankali ya bayyana ƙarara akan fuskokin su,da sauri mahaifin Afrah ya ƙarasa wajen su
"Hajiya mai ya ke faruwa ?"  Cewar mahaifin Afrah hankalin sa a matuÆ™ar tashe
" Alhaji ina kuwa lafiya mun nemi Afrah sama ko kasa a cikin gidan nan mun rasa" ta faÉ—a cikin fashewa da kuka.
"Innalillahi wa'innailaihi rajiun" mahaifin Afrah ya faÉ—a cikin tsananin tashin hankali sannan ya cigaba da magana 
"A garin yaya hakan ta faru? Ya za'a yi a ce a cikin gidannan an nemi mutum an rasa gaskiya abun da mamaki!".
"To Alhaji ni ya za'a yi na sani, wallahi nima abun ya matuƙar bani mamaki kuma duk inda ya kamata mu duba mun duba a cikin gidannan amma bamu ga Afrah ba,wannan wace kalar masifa ce ace ana saura kwana uku biki an nemi amarya an rasa" Mom ta ƙarashe maganar cikin karyewar murya.
Shiru mahaifin Afrah yayi na wani lokaci kafin daga baya kuma yace.
"Shikennan yanzu bara naje wajen Æ´an sanda na sanar da su".
"Amma Alhaji ya kamata mu ƙira Anwar mu sanar da shi halin da ake ciki shima ya sani a matsayin shi na wanda zai auri Afrah ɗin".
Saurin dakatar da ita Mahaifin Afrah É—in yayi sannan yace
"A'a ba za'a yi haka ba, yanzu ki bari muje wajen ƴan sandan muji abun da zasu ce tukunna"ya faɗa yana juyawa tare da nufar wajen motar shi, da sauri wani yayan Afrah wanda ake ƙira da Aliyu ya bi bayan shi.
Gudun da Aliyu É—in yake a titin shi ya sanya basu wani É—auki tsawon lokaci ba suka isa police station É—in.
Kai tsaye office É—in DPO suka nufa inda basu wani tsaya É“ata lokaci ba suka zayyane mishi abun da yake faruwa.
Shima DPO É—in sosai É“atan Afrah É—in ya tsaya mishi a rai domin kuwa wannan abu da É—aure kai yake,a hankali ya É—ago kan shi yana juya biron da yake hannun shi sannan ya kalli su Aliyu É—in yace.
"Amma ranka ya daɗe wannan auren da zaku yiwa ƴarku da son ranta ne ko kuwa zaɓin kune?".
Wani murmushin takaici mahaifin Afrah É—in yayi sannan yace.
"DPO meyasa kamun wannan tambayar?"
"Ka fara bani amsar tambaya ta tukunna kafin ka jefa mun wata tambayar" Cewar DPO É—in yana kafe mahaifin su Afrah É—in da ido.
"Tabbas da son ranta za'a yi wannan auren asali ma zaɓin ta ne ba zaɓin wani ba".
Shiru DPO É—in ya sake yi kamar mai nazarin wani abu sannan ya dube su yace.
"Shikennan Alhaji za ku iya tafiya mu kuma inshAllah zamu yi duk mai yiwuwa dan ganin mun nemo inda Afrah take,ina buƙatar photon yarinyar taka idan kuna dashi ko a waya ne ku tura mun,sannan gidan ka ma ku kasance a cikin shiri domin kuwa a kowane lokaci binciken mu zai iya biyowa ta cikin gidan naku. Abu na ƙarshe shine ina son ka bani address da kuma wasu information akan wanda Afrah zata aura shima zamu yi bincike a kanshi domin kuwa a halin yanzu ko kuma baku fice daga cikin suspect ba".
Sosai mahaifin Afrah suka cika da mamakin maganar DPO ɗin har ya buɗi baki zai ce wani abu Aliyu ya dakatar dashi inda ya sanarwa da DPO ɗin duk abun da ya buƙata game da Anwar ɗin.
Ranar gidan su Afrah kwanan zaune suka yi domin kuwa waɗanda suka iya yin Bacci a cikin gidan ƴan ƙalilan ne,kowa ka gani hankalin shi tashe yake.
Washegari kuwa ƙarfe takwas dai-dai ƙiran wayar DPO ya shigo wayar mahaifin Afrah ɗin a lokacin gaba ɗaya ƴan gidan suna hallare a cikin falon gidan sun yi tsumu-tsumu kamar an jiƙa ɓera a buta.
Cikin sauri mahaifin Afrah É—in ya É—aga wayar gabanshi yana dukan uku -uku sannan yayi sallama.
"DPO ya ake ciki fatan dai akwai wani sabon labari?".
"Alhaji gamu a ƙofar gidan ka zamu iya shigowa".Fita Mahaifin Afrah ɗin yayi sannan ya musu iso tun da ya isa inda suke faɗuwar gaban shi ta tsanan ta sakamakon arba da wani abu da yayi an lulluɓe shi da wani farin yadi a ajiye a ƙasa.
"DPO ya ake ciki?" Mahaifin Afrah É—in ya jefawa DPO wannan tambayar cikin tsananin tashin hankali da rawar murya.
"Alhaji mu shiga ciki tukunna domin kuwa maganar ba zata yiwu a nan wajen ba"
Gaba mahaifin Afrah ɗin yayi inda DPO ya umarci wasu ƴan sanda guda uku da su ɗakko wannan abun da yake lulluɓe ɗin sannan suka bi bayan shi suka shiga cikin gidan,a falon gidan suka yada zango inda suka ajiye wannan abun da ba wanda ya san meye a ciki.
"Bisimillah DPO ga wajen zama" Mahaifin Afrah É—in ya faÉ—a yana nuna musu kujera.
"Alhaji ai zama bai kama mu ba tukunna, inspector jamil buÉ—e musu wannan gawar su gani ko an dace"
Daram gaban duk jama'ar cikin falon ya buga jin abun da DPO ɗin ya faɗa,ai basu ƙara tsinkewa da lamarin ba sai da suka yi arba da abun da yake cikin wannan zanin a lulluɓe,take wasu daga cikin mutanen falon suka dinga zubewa suna sumewa masu ƙarfin halin cikin sune kawai suka tsaya a ihu kawai.
 *MANGA* ✍️
 _Comment_ 
 _Share_ 
 _Fisabillillahi_.

Post a Comment

0 Comments