聽聽聽聽聽聽聽聽聽聽聽聽*1 to 5*
聽聽聽聽聽Sauri sauri, gudu gudu haka take hada
tafiyar tata cike da farinciki, kanta dauke da
qaton faranta na shinkafar datake saidawa,
burinta ta isa gida tagayawa inna wannan
albishir din ta saida duka abincin yau ba
duka,fada da hantara
gab da zata sha kwanan gidansu sukayi karo da
wani makwabcinsu bala,kayan dake kanta duk
suka fadi suka xube qasa..
lokaci daya suka durqusa ita da bala yana fadin
kiyi haquri nainah..bansan da xuwanki bane
tace ba komai bala nayi arxiki na siyarda komai
da kajamin duka a gurin inna yau...
yace nasani nainah shiyasa nake baki haquri,
tayi shiru bata qara tankawaba cos surutu is out
of her hobbies, hrsuka gama harhada plates din
akan faranti ya kama mata ta dora akanta ta
fice da sauri
tun a zaure take kwalawa inna kira..inna! inna!!!
inna na xaune a tsakar gidan tana jinta amma
bata amsaba hr lokacin da tashigo ta ajiye
farantin qasa taxo ta durqusa gabanta fuskarta
da murmushi jikinta hr rawa yake ta ciro kudin
ta miqa mata
inna gashi ki duba duka na siyar kuma ko naira
bata fadi ba...tayi shiru sakamakon wani kallon
da inna kebinta dashi..
tace nainah meyasami wancan kaya nagansu da
qasa...
nainah taja baya cikin jin tsoro dan xata iya
kaimata duka kowane lokaci
tace inna munyi kaura da bala ne shine kayan
suka xube amma bari na wanke, ta tashi jikinta
na rawa idanunta sun cika da kwallah ta ajiye
kudin qasa kusa da inna ta nufi inda farantin
kayan..
bahijja ta shigo gidan kanta dauke da qaton
bokiti na ruwa da kyar ta iya saukeshi ta dirke a
kusa da nainah tana fadin mexakiwa kayanne?
tace anty bahijja xan wankene sun fadi sunyi
qasa..
tace kibarsu inwanke nainah, ina zaki iya
wannan a.....inna ta katseta
ke bahijja kibarta ta wanke wadannan kayan
baxa'ace kamar nainah na dora mata tallah
taxomin dasu da qasa ba ta rainanine...
bahijja tayi rau rau da idanu tana kallon inna
tace inna nainah baxata iya wankesuba, nixan
wanke mata taje ta huta taci abinci dan Allah
inna ki tausayamata..
inna tace ba batun hutu a tare daku, baxaku
huta ni naje nema maku kudi ba dole ku xaku
nemominsu kuma ta dalilinku sai nayi kudi sai
nayi suna a duniya sai kowa yasan dani
INNA.......
Nainah tace anti bahijja kibari na wanke xn
iya...tace tor ta juya inna tace keee! bahijja kixo
ki sharemin duka gidannan kana ki dora girki.....
ta juyo a galabaice tana kallonta
tace dan Allah kibarni na zauna ko kadanne
bayana har ciwo yakemin inna..
tace eyeeee lallai bahijja yau nikikewa musu
tunda kinga kin kusa girmana ko...
ta girgixa kanta tana kallonta idanunta taf da
hawaye...tace tor maxa kidauki tsintsiya ina
jiranki, ina yasir shi kuma, ya fito jikinsa a
sanyaye yana fadin gani inna
tace maxa maxa kafita shago na hanama xaman
gida bakaji bnsan amfaninkaba anan shago
nabaka tsaro ba tsaron gidaba..
yace inna jira nake agama abincine inajin yunwa
sosai bnci komai ba duk yau kinsani
tace tor ina ruwana ubanka ya samo yabanine?
nainah ta juyo tana kallonta idanunta sunyi
jawur saboda kuka tace inna nima inajin yunwa
tun kokon safe bnci komaiba
cikin tsananin fushi ta soma fada
tor ni xakucine ko rayuwata xn dauka na baku
tunda ni uwarkuce,ubanku ya kawo abincine
bana son shashanci wlhy kuka batamin rai sai
inyi maku dukan tsiya...
nainah najin haka ta juya da sauri yasir kuwa
fita yayi cike da tausayin yar qanwartasu itama
bahijjah tana kuka take shara badon komai ba
sai dan tausayin qannenta biyu yasir da nainah
dama mahaifiyarsu na raye.......
ASALINSU
Yan maidugurine irin buxayennen, xama yaxo
dasu katsina, baffa shine mahaifinsu yana da
mata biyu inna ce babba sai ummansu wadda
take da yara uku bahijja ta farko sai yasir da
autarsu nainah.
umman ta rasu tun lokacin haihuwa nainah sai
renonta ya dawo hannun bahijja acewar inna
baxata iya renon abinda bata haifaba dama ita
bata haihuwa fitinarta yasanyawa inna hawan
jini hr yayi mata yawa...
inna irin mutanen nanne masu biyar malamai da
haka ta siye xuciyar baffa yake matuqar
tsoronta duk abinda tace hakane bayamata
gardama shiyasa take yanda takeso a gidan
take mulkin kowa a gidan...
[5:48PM, 8/23/2016] Pherty馃懐: tariga ta qudira
aranta tunda bata haifa ba sai ta wulaqanta
rayuwar ya'yan uku,
A yanxu Nainah is 15 in s.s1 boarding skul
takeyi idan tana gida tana xuwa tallah ko kuma
raino,akoda yaushe batada lokacin kanta, tana
xuwa raino dan samawa kanta kudin xuwa
makaranta baffanta baida kudi inna kuwa komai
bata bata haka take turata skul boarding dan ma
tabarta tanayi acewar inna daso samune tafison
nainah ta xauna gida ta cigaba dayimata
tallah....
bahijja tasamu ta gama tata kuma duk wanda
xaifito neman aurenta bata bari wai dole sai
tafita taje tayi karuwanci takawo mata kudi haka
takeson rayuwar ya'yan ta lalace
a duk lokacin da nainah xata koma skul idan taje
tasha xata shiga mota takesamun baffanta
tsaye yana jiranta saboda inna bata bari yaba
nainah komai sai gyadar dayake noma _can you
imagine yanda xaa tura yaro boarding ba abinci
ba kudi sai gyada fisabilillah_
autana Allah ya kaiki lfy ya dawo dake lfy kici
gaba da addua kinji
ta share hawayen fuskarta tana kallonsa
tor baffa......yaciro kudi dari biyu tsohuwa
dunqule jikinsa har rawa yake yace gashi auta
kinsan banda kudi bana aikin komai sai noma da
zarar nasami kudi xn aikomaki kinji....
ta girgixa kanta tana kallon kudi
kada ka damu baffa jiya majeed yabani kudi da
abinci,ta tsugunna ta bude masa jakarta tana
nunamasa,garine da qanxo sai sugar,quli,sabulai
da sachet din madara irinta goma goma dinnan,
sai dari biyar...
tace anty bahijja ta boyemin maqota kada inna
tagani ta amshe shine yau da safe tabani..
ya share yawayensa yana sanyawa majeed
albarka a xuciyarsa xaije yayi masa godiya ya
qara jaddadamasa indai yana raye nainah
tasashe matarsace halaq malaq.....
ta dauki jakar ta rungume ajikinta tana kallonsa
baffa motar xata tashi natafi kamin addua
yace Allah ya maki albarka nainah sai
kindawo...
ta juya tana hawaye shima yanavhawaye yake
kallonta harta shige motar suka tashi.....
*馃吙herty novels馃摎*
[15:03, 9/5/2016] 鈥�+234 813 535 7888鈥�:
(8/25/2016) Pherty馃帳馃懐
*NAINAH.....馃懓馃徎*
*漏Fertymerh xarah馃挒*
聽聽聽聽聽聽聽聽聽*6 to 10*
聽聽聽聽聽Haka rayuwarsu ke cigaba da tfy cike
da quncin rayuwa tsakanin yaran uku da
mahaifinsu baffa tunda an masu fin qarfi kwata
kwata inna tafi qarfinsu basu da ikon komai a
gidan haka baffa bai isa yasa ko ya hanata duk
abinda tayiwa yaran ba tunda shima baa barshi
ba......
Abdul-majeed shine jigon rayuwar nainah
yanasonta yana taimaka mata yana baqincikin
halin da nainah take ciki shike taimakamata yi
mata provision siyamata duk abinda takeso duk
dashima ba wani qarfine dashiba shima ga
karatu ga rashin wadata gwargwado yana
qoqartawa wajen kula da nainah shiyasa ma ya
nema mata aikin reno saboda tariqa samun
albashi tana buqatarta amma da xaran ta karbo
inna ke amshewa kuma ko kwandala baxata
bata ba inma tabata cikin dubu uku xata bata
naira ashirin acewarta mexatayi da kudi uban
mexataci dasu...
Nainah ta taso da tsanar inna axuciyarta tsana
mai tsanani domin ko sau daya inna bata taba
sanyasu a hanya dai dai ba sai dai tasa su
kaucewa hanya,bayan yayyunta yasir da Bahijja
sai baffanta da Majeed suka dai tasani
masoyanta suka dai takeso da tausayi kuma
suka dai takejin xata taimakawa a rayuwa....
*
Gidane na gani na fada a bada labari, katafaren
harabar gidan an kakkafa canopies da kujeru na
alfarma gidan cike yake da gawurtattu kuma
tsofaffin yan kasuwa da yan siyasar nigeria
wadanda suka dade ana damawa dasu a siyasa
daga cikin nigeria da wajenta,
abokan huladarsa na kasuwanci duka sun
hallara, manya manya motocine keke napep
babura da kekuna birjik ciki da wajen gidan
musamman sunxo domin taya *SANATOR
MOH'D KAITA* murna cin siyasarsa...
kowa kagani cikin farinciki da nishadi yake anata
shige da fice domin fitarda kabakan abinci iri iri
tun daga namu na nigeria,hausawa,igbo,
yoruba,arabian dama turai馃構babu irin wadanda
ba'a fito dasuba kowa ya cika tumbinsa anyi
fanfan...
Nainah na daya daga cikin mutanen danaxo
domin taya baban ubangidanta murna ranar
ansami abinda akeso su inna ankwashi abinci iri
iri ankai gida.....
Alhaji Mohd kaita haifaffen dan Katsina ne a
qaramar hukumar kaita...mutum ne mai arxikin
gaske baida girman kai yana da kyakkyawar
xuciya da fauwala al'amura ga ubangijinsa,abin
duniya baya rudarsa shiyasa talakawa kesonsa
shima yake sonsu.
Matarsa daya Hajiya Maryam wadda suke kira
da hajiya sai ya'yansu uku mata biyu namiji
daya.... R谩uda itace babba tayi aure tana da
yaro daya jafar,sai Mus'ab wanda shi kebimata
sai yar autarsu fauxiya dabatafi 10yrs
*MUS'AB* ya fito daga xuriar Alhaji Mohd kaita
shine kadai yaronsa a duniya bayan
matan,yanada mata daya Mufida da yar'su
Sulaimi wacce nainah ke raino watanta goma
tana koyon tfy ayanxu.
Matashine mai shekara 27,idan kaganshi ma
baxakace yanada aure ba yarone sosai
Mahaifinsa yayi masa aure da 25 ganin kansa ba
wuri daya ba game da mata sannan yanason
yaronsa da tarbiya bayason ya lalace da rayuwar
mata shiyasa yayi mass auren wuri ko ince
auren gata da mufida diyar qanwarsa..
mus'ab bayason auren amma ya karba dan bai
iya musu da mahaifinsa sai dai bayason halin
mufida ko kadan batada nutsuwa tafiye tsiwa ga
kuri ga shegen son jiki komai sai kai aiki ko
wurin shimfida bata tabuka komai haka xai qare
bidirinsa yaaa tsaki cike da takaici yatashi
batare da ya gamsuba,sannan gatada mugun
kishin tsiya ko masu aikinta bata bari sugansh
tana kafkaf dasui kada a kwacemata shi ko
friends dinta da yawa basu sanshiba
wasu kuma a pics kawai suka sanshi ko gidan
sukazo indai yana gidan hankalinta baya
kwantawa har saitayi masa magana ya fita ta
falonsa,xai fice yana girgixa kansa fuskarsa
dauke da.murmushin hali irin mufida,bata yarda
da kowacce mace ba indai akansane kofita zaiyi
da dare sai ta hadashi da qanwarsa fauxiya wai
karya biya inda wata馃槀ko gida zaije gaida
iyayensa bata yarda...
Cikakken matashi dan shekara ashirin da bakwai
yanada wata irin halitta da kalar fat mai daukar
hankali da fisgo xuciya daga garesa musamman
daga fitinannun matan da sukasan qirar namijin
duniya,
dogone wankan tarwada mai ginannan jinkin da
babu qiba babu rama a jikinsa,kamannin uwa da
ubane suka cakude suka bada surar wannan
giant mai sanya xuciyar diya mace cikin
soyayya ta babu gaira babu dalili,idanunsa kadai
suna narkarda xuciyar yan mata shiyasa mufida
take kaffa kaffa da abinta batason kowacce
mace ta rabi jikin mijinta.
yana yanda yakeso yashiga mota mai tsada ya
sanya mai tsada ya taka mai tsada yaci mai
kyau da tsada komai bla...bla... mai tsada
Bashida wata rayuwa data wuce ta jin dadi
amma fa akwai addini baya wasa da sallah ko
kadan Kamar ynda ya tashi Ya sami mahaifinsu
Ya tsare masu ita,sai dai yan'mata kam akwai
su bawai wai yana Nemansu bane suke
nemansa, Duk wannan tsaron da mufida ke
bashi a gida bata San da waje ba馃槀
Duk wata yar 'mai kudi da keji da kanta wurin
kyau aji da ilimi ba irin wadda baiyi yayinta ba
Ya kyaleta sannan ba kalar Macce Mai kyau
fara ko baqa, gajera ko doguwa da Mus'ab baiyi
yayinta ba Ya xubar....
Hr gobe mata na binsa yana masu ynda yaga
dama Dan yasan masifaffiyar matar shi Mai
kishin tsiya baxata barshi ya shigo da wata
mace a gidan da sunan aure ba,shiyasa yake
holewarsa a waje batare da sanin Taba,
Acewarsa shi ynxu Ya gaji da yan'mata wai
kyawawa sun qare, masu ajin ma sun qare
shiyasa Idan bai nuna sha'awa ga mace ba ta
kawo kanta garesa wulaqantata yake shiyasa
yakeda kyankyami akan mata bai taba kusantar
wata mace ba bayan mufida baya xina Duk
xamansa da mace ya rungumeta, kiss, romance
聽is nothing to him馃檮
Skul dinsu daya da mufida Tana hada degree
dinta ynxu ,shikuma ynxu Ya fara masters dinsa,
Tare suke fita Skul wataran a mota daya Shida
ita sai mai rainon sulaimi wato Nainah ta shiga
mota daban driver yakaita Kada wai ta Kalle
mata miji馃槀
Duk sanda batare xasujeba Idan tym din
lectures dinsu ba daya xai tafiyarsa ita kuma
tashiga mota daya da Nainah, bai taba haduwa
da Nainah ba......
*馃吙herty novels馃摑*
[18:27, 9/7/2016] ameerouq: [26/08, 10:12 a.m.]
Pherty馃帳馃懐: *Nainah.... 馃懓馃徎*
*漏Fertymerh xarah 馃挒*
聽聽聽聽聽聽聽*11 to 15*
聽聽聽聽聽Sauri take tana qarawa tana tafe
Tana share hawayen fuskarta saboda dukan da
Inna tayimata safiyar yau Dan kawai ta makara
bata tashi da wuri ba, gashi kuma tayi lattin
xuwa wurin aikinta,
Tafiyar minti talatin tayi a qafa kafin ta qarasa
gidan, flat ne hawa daya Wanda aka gina da red
bricks wato Jan bulo,irin tsarin gidajen ingila
furanni sunyi yawa gidan, rumfa daga sama hr
qasa sannan ga springs na bubbugowa daga
cikin dutse .....
Tana shiga cikin falon ta ci Karo da mufida
fuskarta a murtuqe, gabanta yayi mummunan
faduwa ta durqusa qasa tana fadin
Anty ina kwana?
Tace Ke Nainah karki maidani wata shashasha
aiki na daukeki Idan baxaki iya bane Ki gayamin
na sallameki akwai mutane da yawa dake
neman aikin.
Idanun Nainah sukayi rau rau hawaye fal a
idonta
Tace kiyi haquri Anty baxan qara makara ba dan
Allah Ki yafemin 馃憦馃徎
Taja tsaki Tana fadin ku talakawan nan kamar
gareku aka somajin kalmar haquri, ta juya,
Nainah tace Anty ina sulaimi?
Tana gun mahaifinta idan ya gama wasa da ita
xn kawo maki ita kuma Ki fitar min daga falo
tun mijina bai fito ba,
Da sauri Nainah tabar falon, mufida taja dogon
tsaki hannuwanta a qugunta tana kallonta hrta
fice tana jin haushin Nainah sosai ba dan komai
ba sai dan kyawunta,
Duk da yarinyar na cikin talauci da rashin samun
kulawa kyawunta bai taba gushewa ba, 聽
kasancewarta buxuwa take da fari sosai kamar
Ja, tana da manyan idanuwa da dogon hanci,
bakinta dan qaramine jawur dashi kamar tasa
jan baki amma haka halittarsa take, 聽gashinta
shine yafi daukar hankali, ga tsawo ga cika
kuma baqi sosai, lokacin da mufida taga gashin
Nainah sai da ta tsorata, bama mufida ba hr
Inna tsoron gashinta take, shiyasa mufida Ke
kishin Nainah sosai hrtake kwankwanto anya ba
aljana bace ita komai tanada?
Bahijja ma haka take sai dai Nainah tafita gashi
da hasken fata sosai, yasir ma da yake namiji
daka ganshi kasan ciki daya suka fito dasu
Nainah suna da kamanni sosai na mahaifiyarsu
hrdai Nainah.
Bayan fitowar Nainah ta nufi inda masu aikin
gidan ke xama, ta gaidasu kafin ta sami guri ta
xauna, hajjo yar dattijuwa tana cikin masu girki
ta matso kusa da Nainah....
Yar'nan mai ya hana maki xuwa da wuri hajiya
na ta fada? Nainah ta janyo hannun tsohuwar
suka matsa daga gefe Tana girmama tsohuwar
dn tana sonta sosai,
Tace hajjo kinga yau ma Inna tayimin duka ta
hanamin Karin safe dan kawai na makara ban
tashi da wuri ba, Ya Yaye mata bayanta duk yayi
shatin bulala rudu-rudu abinka da farin mutum
duk bayanta yayi jawur, hajjo ta girgixa kanta
cike da takaici
Tace kiyi haquri Nainah kibarta da Allah
haqqinku Dana mahaifinku ma Ya isheta ganin
isharar duniya, Ki daina kukan haka idanunki
sunyi jawur, Nainah ta share hawayen fuskarta
da gefen dan kwalinta,
Hajjo tace waina na nan na ajiye maki xo muje
kici, ta juya Nainah nabi bayanta cike da qaunar
tsohuwar,
Ta matsa kadan daga su ige dake gyaran kifi ta
xauna ta soma ci suna hira sama sama cos
batason surutu ko kadan, bata dauki wani lokaci
sosai ba ta cinye tas, 聽hajjo taxo da ruwa a
bokiti
Tace taso Nainah tun aiki baiyi yawa ba na
wanke maki Wannan Kan, tubarakallah gaki da
gashi hr baya bakya gyaransa ynxu fa ke kin
girma kin xama budurwa yakamata ace kina
tsabtace jikinki,
Nainah ta tashi Tana warware tubkar gashin
kanta wnda da kyar bahijja ta iya daure mata
shi, Duk wurin suka Xuba mata idanu kowa da
abinda yake saqawa a xuciyarsa game da
gashin, ta tsugunna hajjo ta wanke shi fes sai
sheqi yakeyi,
Tace kije dakinmu damuke kwana akwai toilet
aciki kiyi wanka Ki taje kan Ki shafeshi da mai,
Tace hajjo bnda kayan sanyawa
Tace akwai towel aciki Ki daura, kisanya
hijabina na wanke maki kayan Idan sun bushe ki
sanya kafin akawo maki raino.
[26/08, 10:40 a.m.] Pherty馃帳馃懐: Nainah
kallon tsohuwar take, itace mutum ta biyu
bayan majeed dake nuna mata qauna haka, da
hanxari taje tacire ta dauro towel bayan ta
xumbula qaton hijabi hr qasa taxo ta kawo wa
hajjo Kayan........
Ya fito dauke da sulaimi daga part dinsa Ya nufi
part din mufida bata nan Ya nufi Dakinta bata
nan, jin motsin ruwa a toilet Ya tabbatar masa
tana ciki tana wanka,
Ya juya Ya nufi part din masu aiki dauke da
sulaimi akayi sa'a Duk suna kitchen suwaiba ce
kawai Ke wanke wanke
Yace keee ina mai rainon sulaimi? Jikinta 聽na
rawa ta nuna masa dakin da Nainah take ciki,
yaja dogon tsaki Ya nufi dakin ita kuma Tabishi
da kallo Tana fadi 聽a ranta ashe haka yake da
kyawu shiyasa hjy bata bari muganshi?
Batare da tunanin komai ba Ya fada dakin da
sallama, Nainah na tsaye tana taje kanta duk Ya
xubo bayanta, towel ne ajikinta jin sallamar 聽
namiji Ya sanyata qin juyowa sai dai ta amsa
Sallamar qasan maqoshinta Wanda ba lallai
bane Ya jiyo,
Shi kuma mutuwar tsaye yayi jikinsa hr rawa
yake saboda tsabar rudewa da ganin gashinta,
Duk matan da yake gani bai taba ganin mai irin
gashinnan ba, bugu da qari hasken 聽fatarta Ya
qara Jan hankalinsa,
Jin shiru a xaton ta kowaye Ya fita ya sanyata
juyowa idanunta na sauka akan yatsun
qafafunsa sai ta juya da Sauri batare data Kalli
fuskarsa ba, hankalinta a tashe ko waye miye
dalilinsa na tsayuwa bayanta? Jikinta na soma
rawa kamar daga sama taji muryarsa mai sanyin
gske yana fadin
Ga sulaimi nan, ya ajiyeta a saman gado Ya juya
da Sauri Ya fice xuciyarsa na harbawa,
Sai da taji bugawar qofa sannan ta sauke ajiyar
xuciya ta juyo tana kallon sulaimi, aikuwa tana
ganinta ta wangale baki tana dariya Tana tsalle
hade da miqo mata hannu alamar ta dauketa....
*馃吙herty novels馃摑*
[18:27, 9/7/2016] ameerouq: [8/26, 5:02 PM]
Pherty馃帳馃懐: *NAINAH......馃懓馃徎*
*漏Fertymerh xarah 馃挒*
聽聽聽聽聽聽聽聽聽*16 to 20*
聽聽聽聽聽Yana fita dakin Ya nufi part din
mufida Duk jikinsa a sanyaye hannuwansa goye
a bayansa Ya shigo falonta dai dai lokacin Tana
bude warmers din dake kan dinning, ta tsura
masa ido Tana kallonsa cike da fargaba
'cwt sashen masu aiki naga Ka fito, Meya
Kaika?
'naje Kai sulaimi ne, ina sulaimi ta qara tmbyrsa,
'na ajiyeta akan gado, tayi shiru tana kallonsa
Yace naga wata farar mace mufida ita kuma
wacece?
Nan da nan xuciyarta na soma bugawa Allah
yasa ba Nainah bace yagani, amma data tuna
akwai fararen turawa dake masu dishes
yasanyata jin sanyi gashi kuma Yace akan gado
ya ajiyeta hakan na nufin baiga Nainah ba tunda
bata xama dkin masu aiki nariga na ware mata
Nata daban itada sulaimi inda kayan wasan ta
Ke ciki,
Ta dubesa yana tsaye Ya xuba duka hannayensa
a aljihunsa ya Kafe ta da narkakkun idanuwansa
dake qara mata wutar sonsa,
Tace bana son kana xuwa can dn ba huruminka
bane,
Bai tankataba Ya nufi bedroom dinsu,tabi
bayansa bakin gado ya xauna xuciyarsa na
ingixashi akan yaje Ya qara ganinta Domin ynxu
Ta xamo hasken xuciyarsa *HASKENA* Ya a fili
a xatonsa a xuciyarsa 聽yayi mgnr jin kawai yayi
mufida
Tace me kake cewa Mus'ab, Ya Dan dubeta
yana fadin me kika ji nace?
' *Haskena* Naji Ka fada, Ya tashi fuska a daure
'Tor Idan nace haskena me nake nufi? Tayi shiru
ba amsa Dan batasan me yake nufi ba, yaja
dogon tsaki Ya fice itama ranta a bace ta nufi
dakin sulaimi inda Nainah, ta Sameta Sanye da
qaton hijab ta Dora sulaimi akan keke Tana
turata yarinyar sai dariya take馃槀,ynda Nainah
taga shigowar mufida yasa gabanta faduwa
'Tace Ke Abban sulaimi yabawa sulaimine?
' a'ah Anty akan gado na dauketa
'Tor Ke kin ganshi ne? 聽Nan ma Ta girgixa
kanta da Sauri tana fadin bn ganshi ba hr yau
bnsan kamanin sa ba, 聽aranta taji dadi da ba
Nainah ya gani ba a fili taja dogon tsaki Tana
kallonta a wulaqance
'akan wane dalili daxaki San kamaninsa
'a'ah Anty ina nufin bn sanshi bane gabaki daya,
ta fice fuuuu Nainah tabita da kallo kenan
mijintane yashigo kawo sulaimi daxu amma taso
taganshi taga meke jikinsa da fuskarsa da
mufida Ke tsananin kishi haka,
Tafin qafafunsa kawai tagani yanada dogayen
yatsu shi Kadai xata iya tunawa, mtsew da kin
daina wahalar da kanki indai nice majeed Ya
fiye min komai a rayuwarnan nafi sonsa da duk
wani da'namiji a duniyarnan, ta dubi sulaimi tana
fadin Allah yasa karkiyi halin uwarki saboda Duk
kamaninta kika biyo,ta dubi yatsun qafafunta
tace suma na mamankine, na Babanki sunfi nata
kyau,
Ta dauketa ta kwantar da ita a saman gado
hade da cusa mata feeder a bakinta ta soma
shafa jikinta Tana jijjigata akan tayi barci, bata
jima ba kuwa barcin Ya dauketa itama Nainah ta
qara gyara kwanciyarta domin samun barcinta
daman a gidan kawai take samun barcin rana
idan a gidane a gaban inna Waye ubanta ta
xauna ta huta balle kwanciya.
[8/26, 7:55 PM] Pherty馃帳馃懐: Yana fita gidan
inda Fahad Ya nufa Ya sami surayya 聽matarsa
xaune a falo, Ya xauna cike da damuwa yana
kallonta,
'ina abokina?
'yana ciki
'kirashi pls, ta tashi Tana fadin meke damunka
ne, naganka wani iri ba ynda na Saba ganinka
ba,
Yaja dogon tsaki Yana fadin tsiyarku kenan ku
mata sai Kuce ku komai sai kunji, dawo Banaso
Ki kirasa, Ya tashi ya nufi part din Fahad,
Ta soma dariya Tana fadin na mufeedah bada
kanka a sare 馃榾
Yaji kamar ta soka masa kibiya a qirji , a fusace
Ya shiga dakin suna 聽hada ido da Fahad
'Yace kajawa matarka kunne wlhy xn fasa mata
baki馃槧
'Fahad Yace Tor namamajo, 聽mgnr ta qara
tunxurashi sosai cike da bacin rai yake kallonsa
'kaxo gidana kuma kace xaka fasawa matata
baki akan wane dalili ko ka dauka yan matanka
ne mema kaxoyi da tsakar rana ynxu ko xakaje
lectures ne? Mtsew ya xauna bakin gadon yana
kallon Fahad Kai tsaye Ya warware masa komai,
'Kai Baka tunanin qawartace taje wanka acan
gudun karta yi anata kaxo ka ganta kasan fa
kishi irin na mufeedah ko qawayenta bata bari
ba,
'bana tunanin qawartace cos Wannan fa
yarinyace mufida ta girmeta sannan Dana
tambyeta farar mace komai bataceba, inaji mai
rainon sulaimi ce amma abokina dama akwai
talakawa kyawawa 聽haka?
'subhanallah Fahad Ya fada yana kallonsa Yace
'karkayi ixgili fa,
Mus'ab Yace kasan ynda na tsani talaka badan
komai ba sai Dan mugun kwadayinsu ka dauki
dawainiyar mata sannan ka dauki na iyaye Kai
hrda ma danginsu sannan ga roqo suyita
damunka ynxu abokina ka gayamin mafita ina
son yarinyar nan Wlhy I Mean it xn iya rasa
komai nawa akanta wai Kaga ma gashintane
chabdi馃
'Fahad Yace yakai na hema ne?
_'pls stop joking seriously I mean it_ Shawara
xaka bani,
'Ya sunanta Fahad Ya tamby,
'bansan sunanta ba amma na sanya mata wani
sunan daban
'wane suna Ya tambysa cike da mamaki,
idanunsa akan Fahad Yace _*HASKENA I mean
hasken xuciyata hasken idaniyata,*_
Fahad Ya kyalkyace da dariya lallai ma amma
naso ganin Hasken Kaita, naga dame tafi sauran
naga meya 聽Rudaka akanta kake abinda Baka
taba Yiba akan mace,
Murmushi yayi yana fadin baxaka gane 聽bane
*haskena* ta dabance,
'Fahad Yace abinda xakayi Gobe ka dauki
sulaimi kayi wasa da ita kamar yau sai kabawa
mufeedah ita Idan ta Kaima mai rainon ta dawo
sai ka xare mata idanu akan sai ta Kira mai
rainon sulaimi kaga anan xaka ganta koma me
xai biyo baya kaida mufida ba ruwana...
Ya tuntsire da dariya hade da kaiwa Fahad duka
a baya
'shege abokina kaifa akwai idea amma da haka
mata Ke 聽cutuwarka
'haba Kaita kayi shiru 聽Kar surayya tajiyo pls...
Da murmushi Ya fice yana fadin sai Kajini
mayen surayya, 聽Fahad Ya rakosa hr gun
motarsa suna tattauna mgnr.
Haka kuwa akayi washe garin ranar Ya xare
mata idanu akan sai ta Kira mai rainon sulaimi,
'mai yasa xn kirata ,mexa tayima ne, kagayamin
sai inyima...... 聽Duk ta rude jin Nainah xataga
mijinta,
Wata tsawa da yayi mata batasan lokacin da ta
fice ta nufi dakin sulaimi ba, bata taba ganin
fushi da bacin rai mai Tsanani ba kamar wnda
tagani yau akan kyakkyawar fuskarsa.
*馃吙herty novels 馃摑*
[18:27, 9/7/2016] ameerouq: [8/26, 11:17 PM]
Pherty馃帳馃懐: *NAINAH.... 馃懓馃徎*
*漏Fertymerh xarah馃挒*
聽聽聽聽聽聽聽聽*21 to 25*
聽聽聽聽聽聽聽聽Xuciyarta kamar zata fashe
saboda tsananin tsoron ynda mijinta xai ga
Nainah ,ta murda qofar dakin sulaimi ta shiga
Tana ganin lami xaune da sulaimi ta saki ajiyar
xuciya hrda murmushi a fuskarta kwata kwata ta
manta Jiya da Nainah xataje gida ta gayamata
baxata sami damar xuwa ba cos batajin dadin
jikinta
'dauko sulaimi kibiyoni lami, ta juya koda ta isa
falon yana tsaye yana tsaye idanunsa akan qofa
suka shigo, ya saki wani malalacin tsaki cike da
qunci,
_'mufeedah tell her to go back please_ Ya Juya
Ya fice ta bisa da kallo batasan dalilin abin nan
da yake ba,
Ransa a bace ya kira Fahad yake sanardashi
komai
_'continue praying and searching you will see
her_ indai Tana gidan, inka fito Anjima xamuyi
mgnr,
'shikenan Ya Tsinke wayar,
Yana tuna fararen idanuwanta Manya dasu, yaga
bakinta qaramine kuma jawur ya lumshe
idanuwansa hade da xira hannuwansa cikin
sumar kansa *haskena* ya fada a hankali.
*
Nainah kuwa tun bayan barinta gidan da xaxxabi
ta nufi gida amma inna bata Bartaba sai da
tasanyata 聽wankin kayanta kaf,
Da dare saboda xafin jikinta yasanya bahijja
tausa. mata jiki da tsuma, ganin ynda haqoranta
da labbanta Ke rawa yasanya bahijja ta Kira
baffa,ya taba jikin Nainah xafi rau, gashi
Bashida wani kudi dari da hamsin ne kawai,
'bara naje chemist na siyo mata mgn, ya fice
bahijja ta rungumo kanta Yasir ya cigaba da
tausa mata jikinta da tsumma,hr baffa ya dawo
聽da magani suka tadata xaune tasha hade da
Kora ruwan tea馃嵉 da yaxo mata dasu ta
kwanta.
Washe garin ranar xaxxabi Ya sauka kadan
amma jikinta Nada xafi kuma tana ganin Jiri,
Tana xaune bahijja na sharar gidan inna ta fito
da farantinta na shinkafa da wake da mai da
yaji, ta dire gaban Nainah tana fadin
''tunda baxakije rainoba kina mana baqin ciki da
abinci mai dadi Tor Kitashi i
Kije talla kuma Ko kwandala Kada ta bata
abincin Naira dubune,bahijja ta tsaida sharar da
takeyi
'inna Nainah bata da lfy kibarta ta huta shiyasa
bataje reno ba,
'Tor ina ruwana da lfyrta talla nace taje Tamin
kuma ko kwandala ta bata Nainah Wlhy sai na
fiddata a jikinki, 聽Nainah ta soma kuka Tana
roqonta, bahijja ta ajiye tsintsiyar Tana kallonta
'inna kibar Nainah ta huta ni xnje maki tallar,
''Inaaa Sam ai Wlhy baxata yiwuba Nainah
xataje Ke kina gida saboda Nainah xn maida
karuwar waje Ke kuma ta gida, taje talla Duk
wnda Ya Tara Tabashi abinda yakeso a jikinta ta
Kawomin kudi, 聽Ke kuma da Ke gida Duk wnda
yaxo siyen abinci Yanuna Ra'ayinsa akanki xaki
bashi Ki kawo min kudi a dakin mahaifiyarku
xaku dinga shiga da samarinku, Wannan kyawun
naku dashi xnyi jari nayi kudi diyan *BUZAYE*
[8/27, 9:57 AM] Pherty馃帳馃懐: Maxa Maxa Ki
tashi tun ban hau kanki da duka ba, 聽Nainah ta
tashi da kyar ga jiri ta dora mata farantin
shinkafar Tana kuka, baffa dake shigowa
'Yace amma Kinsan yarinyar batada lfy kuwa,
kiyi mata uxuri Dan Allah, inna ta riqe haba cike
da mamaki
'Tace yau nasiru ni kake hanawa na aiki
Ya'yanka, tunda bn haifa ba hr ni kake yiwa
gardama akan Nainah to Kai xaka Je min tallar
ne kome?
'Yace Nainah kije Allah na nan baya barci,
'da Karka Barta taje kagani wlhy馃槧
Kuka Nainah keyi sosai ta fito daga gidan jiri
take gani tfy take ko gabanta bata gani batama
San inda take jefa qafafunta 聽ba, bata
ankaraba ta daka wani uban tuntube gabaki
daya itada tiren suka xube qasa, jikinta na soma
kyarma gabanta hr faduwa yake ta tartar
shinkafar sama da batayi qasa ba, mai kam
gabaki daya Ya zube,yajin ne ma bai zube ba
dan yana a Leda,
Hawaye Ke Tsiyaya a idanunta lokacinda ta
tsinkayo bahijja da majeed tafe, ta xauna
Dirshan gaban farantin Tana wani irin kuka,
Bahijja 聽ta dafa ta,.
'Ki xo Nainah ynxu na fito inna bata sani ba naje
na kira majeed xai kaiki amaki allura, cikin kuka
Nainah ta soma mgn
'Anty bahijja inna xata kasheni yau Ki taimakeni
na barar da shinkafarta, bahijja ta xare idanu
Tana kallon abincin dake xube a qasa zuciyarta
na bugawa,
'Ki tashi Nainah abinci baifi rayuwarki ba, Idan
xata dakeki xn tare maki sai dai ta kashemu
tare kixo muje amaki allura,
Da kyar ta tashi bahijja ta dauki faranti majeed
kuwa Ya riqa hannunta suka nufi chemist, aka
mata allura tare da maganin 聽malaria, majeed
Ya biya kudin suka fito, bahijja ta wuce gida da
Sauri su kuma suka nufi Gindin wata bishiya
suka xauna,
'sannu Nainah Allah Ya baki lfy, da kyar ta amsa
tana kallonsa Tana jin sonsa ta ko ina a jikinta,
ya ciro farar takarda Ya bata yana fadin duba
Kigani Nainah kitayamu farin ciki na samu aiki
Abuja qarqashin wani company, xnyi kudi Nainah
na daukeki daga inna, 聽na fitar dake cikin
damuwa da quncin rayuwa Mubar mata garin
muje Abuja,
Ta fadada murmushinta wnda hr fararen
haqoranta sai da suka bayyana, dimple dinta Ya
lotsa
'ina tayaka murna, Allah yasanya albarka,
'Yace Amin *sanyina* Ya riqo hannuwanta xnyi
missing dinki Nainah kin xamo *sanyin
idaniyata, I mean Sanyina*,hr inajin tsaron Idan
naje kada wani Ya kwacemin Ke Ki manta dani,
Ta girgixa kanta Tana murmushi
_'nooo majeed u mean alot to me a duniyarnan,
ba wanda xnso 聽bayan Kai kaine farin cikina
Kai kake bani haske duk runtsin dana tsinci
kaina, pherty ma ta fada kaine jigon rayuwata,
kasa a xuciyarka ni takace ina sonka majeed馃
槏_
Ya sauke ajiyar xuciya yana kallonta
'na yarda da Ke *sanyina* insha Allah da xaran
nadawo xaa fara mgnr aurenmu.....
Ta rufe fuskarta da Tafin hannuwanta cikin jin
kunyarsa, shima dariya yayi yana kallonta
'kafin naje xn baki kudi Ki koma Skul, ilimi fa
jigon rayuwane, ta gyada Kai tana kallonsa
xatayi mgn ta tsinkayo inna tafe fuskarta a
murtuqe馃槨,lokaci daya xuciyar Nainah na
buga....
*馃吙herty novels馃摑*
[18:27, 9/7/2016] ameerouq: [8/28, 7:08 AM]
Pherty馃帳馃懐: *```NAINAH...馃懓馃徎```*
*```Na fertymerh xarah馃挒```*
聽聽聽聽聽聽聽聽聽聽聽*26*
`Ihun da naina ta tsala ta kifar da farantin
shinkafar dake kanta shine ya raxana Majeed,
yaji gabansa ya yanke ya fadi ya juyo da sauri
sai yaga inna dauke da qatuwar bulala ta
cakumo rigar nainah ta baya tana qoqarin 聽
lafta mata ita
`majeed yaxo da sauri ya riqe bulala hade da
fisge nainah daga hannun inna yayinda nainah
taxo a guje ta boye bayansa tana fadin kada
kabari ta dakeni xata kasheni
`inna fadi take hrda kumfar baki tana danna
ashar tace kyaleni da tsinanniyar yarinyar
nan,yau sai na kasheta nixakiyiwa hassarar kudi
sannan ynxu ki xubarmin da abinci?..
`magiyar da majeed yake mata ya sanyata yin
shiru tana huci take kallonsa kamar xakanya
`majeed yace haba inna wacce hassarace ta
sameki haka har xaki manta da ubangijinki?
musulmin kwarai baya mantawa da qalu
innalillahi wa inna ilaihir raji'un duk sanda
masifa ta sameshi, kinata danqara ashar akanta
kina sai kin kasheta meyasa?
`haushinsa yasa inna tsuke fuskarta..malam
wa'axi kakemin ne akan ya'ta nida ya'ta ka
hanamin dukanta miye naka acikine eyeee, ta
fada tana xare masa idanu cikin masifa...
`yace a'ah inna dan Allah kiyi haquri nasan kina
cikin bacin rai da damuwa amma kice qalu inna
lillahi wa inna ilaihir raji'un.
`inna tace yaxanyi dole ince tunda Allah ya
hadani da shegiyar yarinya inna lillahi wa inna
ilaihir raji'un shikenan?馃槨
`majeed yayi murmushi yana fadin yauwa inna
kijira Allah kiga sakayyar da xaiyi miki, ya sanya
hannu a aljihunsa yana fadin nawane kudin inna?
`tana yatsina fuskarta tace dubu dayane, yaciro
dubu biyu ya bata ta karba, yana fadin dan Allah
inna kada ki daki nainah da Allah na
hadaki...tace tor..kawai, ya juya ya kalli nainah
yayi mata murmushi ya fice yanason kawo
farinciki a rayuwar naina tana cikin qunci da
damuwar inna, a ransa kuma fadi yake wata
uwar kenan.
`suna hada ido da inna tayi saurin sunkuyawa
tana kwashe kwanukkan data barar na shinkafa,
inna taja dogon tsaki tace xamu hadu dakene
ina jiranki a gida ta juya da sauri nainah ta dago
tana kallonta cike da fargaba xuciyarta sai
bugawa take kamar xata hudo qirjinta ta fado....
Da sanda ta isa gidan taxo gaban inna ta
durqusa tana kuka take bata haquri, takai mata
rankwashi a Kai tana fadin
'ai tunda kudina sunxo shikenan amma Ki kiyayi
gaba, Nainah ta tashi cike da farin ciki amma
sai me amai yaxo mata lokaci daya Ta matsa
gefen inna tanayi....
Dariya inna ta tashi tanayi Tana tafa
hannayenta
'ni daman nasan ba banxa ba Wannan majeed
din sai ya lalata rayuwarki, haba shiyasa yabani
dubu biyu ynxu saboda yasan abinda yayi Tor
Wlhy baxan yarda ba sai an biyani kudin
shinkafata wadannan kudin iskancin da yayi da
kene,
Nainah komai batace ba tana tsugunne bahijja
na kawo mata ruwa Tana kuskure bakinta
[8/28, 7:42 AM] Pherty馃帳馃懐: Kamar daga
sama suka jiyo murya mufeedah tana sallama
Tana dauke da sulaimi yayinda driver k bayanta
dauke da Leda
Inna na ganinta ta shiga washe baki
'a'ah Maraba da hjy sannunki da xuwa, jikinta na
rawa ta shiga Ta dauko Tabarma taxo ta musu
shimfida suka xauna, bahijja ta riqo Nainah,
atare suka gaidata,
'Nainah ashe jikin yayi tsanani haka, kinje asibiti
kuwa?
Ta girgixa kanta Tana hawaye
Inna Tace ai kudin xuwan asibitin ne babu, Duk
yan canjina na siyamata magani dasu馃
檮,Nainah ta Kalli bahijja ita kuma bahijja kallon
inna take da mamaki,
Sulaimi kuwa Tana ganin Nainah ta rarrafo da
Sauri ta nufeta Tana dariya, mufeedah ma
dariya tayi Tana fadin
'sulaimi bata yarda da lami sai ta rinqa fitina,
nasan Ke take nema, sulaimi na sonki Nainah
shiyasa nake sonki hrna kasa haqura naxo
dubaki,
Nainah ta sunkuyar da kanta Tana kallon
sulaimi,
Mufeedah Tace hrda amai kikeyi kenan, kinci
abinci kuwa? Nan ma Nainah girgixa kanta tayi..
Inna Tace ynxu nabawa yayanta yasir kudi Ya
siyo mata indomie na dafa mata taci 馃檴
'Allah Ya sauwaqe, suka ce Amin.
Ta dubi driver ta Tace duba a ledar akwai fresh
yo dana xo mata dashi yanada sanyi bata tasha,
Ya ciro yaba Nainah,
Ta Karba Jikinta na rawa ta soma sha dama
tana jin yunwa, tasha sosai kana ta ajiye
sauran, inna sai harararta takeyi,
Mufeedah ta tashi ta ciro naira dubu sabuwa
Tana fadin gashi Ki sai wani abu Idan kina
buqata
Inna ta amshi kudin da Sauri tana fadin
'hajiya Wannan kudin baxasu isa xuwa asibitin
ba, 聽mufeedah ta kalleta da mamaki
'kinji nayi mgnr asibiti anan ne? 聽Nainah na
bawa kudin Idan driver Ya maidani gida xaixo Ya
kaita asibiti, 聽Inna bata amsa ba saboda
takaici, bahijja ce ta soma godiya itama Nainah
tayi mata Godiya,
Tace ba komai ta dauki sulaimi hade da miqa
mata ledar Tana fadin
'gashi inji sulaimi kayan dubiya ne, Duk suka
kwashe da dariya bnda inna..
Mufeedah tayi masu sallama ta fice inna nayo
kan Nainah ta shaqureta Tana fadin
'shegiya Dan kwadayi anbaki kika shanye Niban
sha ba, Tor sai kin amayar dashi, bahijja ta
soma Ihu Tana Kiran baffa ganin ta tura
hannunta bakin Nainah hr kakarin amai takeyi,
Shigowar baffa yana fadin subhanallah, abinka
da marar lfy kuwa Ta soma kwararo amai Duk a
jikin inna, ai kuwa Ta dauketa da wani
gigitaccen Mari.....
*馃吙herty novels馃摑*
[18:27, 9/7/2016] ameerouq: [8/28, 11:21 AM]
Pherty馃帳馃懐: *```NAINAH```*馃懓馃徎
*```Fertymerh xarah 馃挒```*
聽聽聽聽聽聽聽聽*27*
聽聽聽聽聽Tayi tangal tangal xata fadi baffa yayi
saurin riqota ,Ransa inyayi dubu Ya bace ya
dago a fusace yana kallon inna xaiyi mgn suna
hada ido ya kasa sai ma wani tsoronta da yaji
Ta xare masa idanu sosai
'kayi magana mana ko xaka Rama matane? 聽
Ya girgixa kansa da Sauri, taja dogon tsaki Ta
fice,
Bahijja ta riqota, baffa ya goge kwallar da ta
xubo masa
'kullum ina addu'a Allah Ya saka maku ku
cigaba da haquri rayuwace, kije Ki gyara mata
Jikinta, ya fice hawaye fal a idanuwansa,
Driver yaxo Ya kaita asibiti akayi treating dinta
hade da magunguna masu tsada Ya maidata
gida....
Kwana biyu ta warke garau ta fara fita
aikinta....
*
Cikin hanxari yake shirinsa morning lecture
yakeda yau itama mufida Tana da lecture
shiyasa take Sauri su fita tare,
A tare sukayi shirinsu suka fito yayi tsaye yana
kallon motocin dake garage daya bayan daya
yana tunanin Wace motar xai shiga yau,
Mufida ta sanya Nainah da sulaimi a dayar
motar driver Ya jasu,
Suma basu jima ba sukabi bayansu, sanda suka
iso hr driver Ya ajiye su Nainah ya juya, kamar
Ance Mus'ab Ya dago Ya tsinkayota goye da
yarinya a bayanta,
Da qarfi yaja birki hade da fadin *haskena*,
kafin mufida tayi mgn tuni Ya fita da Sauri Ya
nufi hanyar da Ya ganta, 聽Duk saurinsa bai
gantaba Duk iya qoqarinsa bai tsinkayeta ba
waige waige Ya Somayi yana neman hanyar da
xai ganta,
Mufida ta qaraso Tana fadin
'menene Mus'ab me kake nufi wai da haskenka?
Mtsew yaja dogon tsaki yana cigaba da waiwaye
ko xai qara tsinkayota kafin ya juya Ya fice
Ransa a bace badan Ya Soba.
[8/28, 6:37 PM] Pherty馃帳馃懐: Ta tabe bakinta
ta fice,
Ya rigata gama lectures,
Sun fito tare da Fahad yana gayamasa abinda
Ya faru da safe, saman mota suka xauna atare
su biyu, sai ga wata farar mace ta wuce ta
gabansu, Fahad Ya juyo da Sauri yana kallonsa
'Kaita naga haskenka fa..., 聽da Sauri Ya juyo
yana kallonsa alamar a ina? Fahad Ya nuna
masa ita, mtsew Mus'ab yaja dogon tsaki yana
fadin
'Wannan fake ce, farinta na bleaching ne, 聽
haskena tafita, _haskena is young not old like
this bitch_,
Fahad Ya kyalkyace da dariya, bayan ya sauko
motar yana fadin
'ga shawara abokina... 聽Mus'ab Ya juyo yana
kallonsa
Yace Wannan hasken taka Tana gidanka believe
me kamar na taba ganin wata farar mace a
gidanka amma ban sami ba ko itace,
Mus'ab Yace ba ita bace cos munada farare
masu aiki a gidan,
Fahad Yace Duk da haka ka gwada Tara duka
masu aikin gidan Maxa da mata kace xakayi
masu kyauta Kaga anan xaka dubata kasan
talakawa da kwadayi kowa xaije,
Mus'ab Ya sauko yana kallonsa
'Wace kyauta xan masu Fahad?
'kaje ka saro dilolin shadda ka raba masu Nixan
tayaka aikin,
Mus'ab yaja numfashi yana fadin shikenan xnyi
muje mu siyo shaddodin, atare suka shiga
motocinsu suka fice...
Da dare maaikatan gidan lbr ya riskesu kowa
murna yake Alhaji Mus'ab Yace xai bawa
kowane ma'aikaci shadda, 聽da abin suka
kwana a Ransu bama kamar Nainah da hrta
gayawa bahijja da Yasir,
Yasir Yace Anty bahijja nasoma gajiya da halin
inna Wannan Karon ta sake dora hannunta akan
Nainah sai dai baffa ya Koreni amma Wlhy xn
Rama mata,
Bahijja ta tabe bakinta Tana fadin Allah shine
gatanmu ,Nainah bata tankaba ta kwanta ta
qagu safiya tayi taje ta karbo shaddar ta bawa
baffanta tasan xaiji dadi kuma ya sanya mata
albarka......
Washe garin ranar, da sassafe Nainah ta fice ta
isa gidan Duk maaikatan gidan sun iso, da Sauri
Ta shiga cikin gidan tasami mufida 聽xaune da
sulaimi, ta
duqa Tana gaidata kana ta karbi sulaimi ta
goyata ta fita waje inda sauran ma'aikatan suke
tsa-tsaye Maxa da mata......
*馃吙herty novels馃摑*
[18:27, 9/7/2016] ameerouq: [8/29, 8:29 PM]
Pherty馃帳馃懐: *NAINAH..... 馃懓馃徎*
*Fertymerh xarah 馃挒*
聽聽聽聽聽聽聽聽聽聽聽*29*
聽聽聽聽聽Nainah na tsaye tare da hajjo mufida
ta xo ta kirata,
Suna shiga falo mufida ta juyo tana kallonta...
'wat a disgrace Nainah kijemin da ya' cikin
talakawa hrkina tsayuwa,
Nainah ta sauko da sulaimi tana fadin
'Anty Ance xaa bada shadda ne shiyasa naje
nabi layi,
'Tor ai kin fisu matsayi a ynxu Nainah, cos kina
rainon sulaimi yar' masu gida, sannan sulaimi na
sonki shiyasa nake ji dake, kije dadin sulaimi
Kicigaba da rainonta ni xn kawo maki shadda
hrma da turmin atampha,
Murmushi Nainah ta saki wanda ya qara fito da
kyawunta dimple dinta Ya lotsa ta dauki sulaimi
tana Godiya ta fice, mufida ta bita da idanu
yarinyar akwai kyau shiyasa baxan bari Mus'ab
Ya ganki ba,
Nainah na kwance sulaimi na gefenta ta sakar
mata kanta tana wasa da gashinta Duk ya baje
jikin sulaimi mufida ta shigo, 聽sai da ta kusan
faduwa saboda raxana, yawan gashin da
tsawonsa na bata tsoro
'Nainah.... Ta Kira sunanta a hankali, Nainah ta
janye gashin ta dago Tana kallonta,
'Ki godewa Allah Nainah kinada halitta mai kyau
baxan boye maki ba ina kishinki fiye da sauran
matan bana so mijina ya ganki, na yarda mijina
yaga kowacce mace a gidannan da qawaye na
amma bnda Ke....., 聽Nainah tayi far.. Da idanu
Tana kallonta
'Anty karki tsaneni Kema saboda mijinki, inna ta
tsanemu Kema karki tsaneni, majeed mean alot
to me ina sonsa fiye da ynda kike son mijinki,
baxan iya xama da kowane namiji a duniyarnan
Idan ba shi ba,
Mufida ta xauna gefenta hade da dafa
kafadunta
'gayamin Meyasa inna ta tsaneku bayan naga
tana sonku Tana kula dake, ba Mahaifiyarka ku
bace?
Nainah ta girgixa kanta Tana hawaye,
'bnsan mamana ba, mamana ta rasu sanda ta
haifeni 馃槩(nan ta bata lbrn komai) mufida ta
tausaya masu sosai tace _I will help u Nainah,_
ynxu kina aji nawa ne?
'S.S 2 ,xnje ynxu due to rashin kudin makaranta
ne bnjeba ynxu hr ana second term but majeed
Yace xaibani kudin,
Mufeedah.. Mufeedah taji murya Mus'ab na
kiranta da Sauri ta tashi Tana fadin ga kayan
nan _we talk later, I will help u insha Allah_, ta
fice.
Sanda suka fito da Fahad duk ma'aikatan suka
nutsu sai gaisuwa suke shikuma fuskarsa a
murtuqe take amma Duk da haka kyawunsa bai
boye ba,
Masu aikin gidan Duk sun xuba idanunsu akan
kyakkyawar fuskarsa yau ne Karo na farko da
suka soma ganinsa wasu kuma sau biyu inka
cire maxan, basuga laifin 聽mufida Dan ta boye
mijinta a ynxu ba,
Fahad Ya dago a fusace ganin shikadai Ke
Rabon Gogan na tsaye Ya fake da yana qirgasu
ne Dan yaga Koxai ga haskensa,
'malam sai ka Sunkuyo mu raba kayan tare ko,
Mus'ab Ya sunkuya fuskarsa ba Walwala cikin
muryar da ba kowa xai jisaba yace
'abokina bngantaba *haskena* bata cikinsu ya
xnyi? 聽Fahad Ya dubesa
' _be strong Abokina, kada ka bari su fuskanci
wani abu pls, we talk later,_
Mus'ab Ya sunkuya suka cigaba da Rabon kayan
badan yaso ba..
Bayan sun gama ne suka nufi bayan gida suka
xauna bisa irin saqaqqun kujerun nan na
gargajiya da ake saqawa da xaren roba,
Wadanda sau tari anfi samunsu a gidajen
manyan masu kudi da kwalli,
Madaidaicin tebur din kaba ne a tsakiyarsu,
Fahad Ya xuba ruwan Coca Cola mai sanyi yana
Kumfar gass,
Ya kafa kofin abakinsa yana sha, sai da yasha
mai isarsa kana ya dubi abokinsa da yayi shiru
yana tunani yace
'oh Allah ka nuna mana *hasken kaita* mu huta,
wai Wannan Wace yarinyace da ta ruda ka haka,
me take dashi wnda sauran matan basuda,
fararen mata nawane 聽a Skul dinmu hrma a
gari gasu kyawawa sai wadda kakeso ka xaba
tunda gaka da kyau da ilimi bugu da qari kudi
Wadanda sune jagorar rayuwar Dan'Adam 聽a
ynxu....
Mus'ab Ya juyo yana kallonsa...,
'tun da na fara ganinta nake mafarki da ita, a
mafarkina ina ganinta cikin wani Hali _olways
crying seeking for help and I need to help her, I
want to be with her, I so much love her Fahad_,
sai ga hawaye na xuba a idanuwansa wnda Ya
sanya Fahad rudewa cikin matsinancin tashin
hankali tunda yake da abokinsa bai taba ganin
hawayensa ba sai yau adalilin mace, macen ma
da batasan yanayi ba, Fahad Ya riqosa
_'be strong abokina, Idan *haskenka* rabonkace
xamu ganta a Skul da gidanan xamu cigaba da
nema, amma Idan kansa Allah Ya taimakeka
akan burinka ka riqa taimakon talakawa Allah
xai taimakeka ka rage tsanarsu pls Mus'ab_
Yayi shiru kawai yana kallon Fahad, Idan Dad
dinsa Ya dawo xaije Ya sanardashi a nemo
masa *haskensa*
[8/29, 8:29 PM] Pherty馃帳馃懐: Da sanyin
marece Nainah tabar gidan bayan ta damqa
sulaimi ga mufida, Kai tsaye gidansu majeed Ta
nufa Ta samesa da mahaifiyarsa iya xaune ta
gaidata hade da ciro turmin atamphar ta bata,
'iya gashi na kawo maki Ki dinka kisa..nasan
xata maki kyau馃槉, iya ta Karba tana dariya
cikin farinciki tana buda atamphar
Majeed Yace 'Nainah ina kika sami atampha, ta
nuna masa shaddar Tana fadin
'gurin aikina aka bani shiyasa nakawo wa iya
Wannan sai in kaiwa baffa shadda...
Iya Tace shine kika bani Tor kefa, ga kuma
bahijja ai Kunfini buqatar Sutura Nainah dubi
kayan dake jikinki馃槩
'iya Ki riqe atamphar na baki Idan na dinka ko
naje da ita gida inna xata karbe ta saida,
gwanda na ganta a jikinki danaje ina ta Karba ta
saida taci kudin...,
'hakane Nainah amma xn baki kudin atamphar,
Nainah ta tashi Tana fadin
'a'ah iya kyauta nayi maki bana son komai
naki...
Tace Tor na gode Nainah Allah Ya maki albarka
ya qara maku haquri da matar baffanku, Idan
majeed Ya dawo daga Abuja xaa sa ranar
bikinku....
Kunya tasa Nainah fita gidan da Sauri tana
murmushi, majeed Yabi bayanta,
Tafe suke cike da jin dadi, sanyin marece da
iskar da ake take qara masu shauqin junansu,
suna tafe suna kallon Sararin samaniya kowane
na jin son Dan uwansa na Ratsa jikinsa,
Ta juyo tana kallonsa
'Yaushe ne tfyr taka?
'Uhmm next week insha Allah, kin matsu naje
ne?
Ta gyada Kai tana kallonsa,
Yaja ya tsaya cike da mamaki,
'saboda bakyasona ynxu?
Tana murmushi tace noooo
'why? Ya tambayeta
'saboda kaje ka dawo da wuri na bar gidan inna,
聽Anty bahijja da yaya Yasir ma subar gidan su
xauna tare damu馃檮馃檴
Ya kyalkyace da dariya lallai Nainah yarinya ce
'Yace Tor shikenan Nainah Allah Ya nuna mana
ranar,
Tace Amin kafin ta dubesa
Ynxu magrib ake neman yi, yakamata kabarni
haka na qarasa,
Oh *sanyina* bn gaji da ganinki ba
'tace kayi haquri,
Yace Tor shikenan Anjima xnxo,
Ta juya Tana fadin _will be waiting for u after
isha'i_, yayi murmushi Ya juya.
Sanda ta iso qofar gidan baffa na xaune yana
arwalla ta bashi shaddar
'baffa gashi aka bamu wurin aikinmu na kawo
ma na baiwa iya atampha, Ya Karba jikinsa na
rawa yana dubawa
'nagode Nainah Allah shi maki albarka na kuma
ji dadin da kika baiwa iya atampha, amma bakya
ganin Idan inna tagani xata karbe,
Nainah ta karbi atamphar Tana fadin kawo na
bada maqota a ajiyema Gobe sai ka Karba ka
Kai dinki Yasir sai ya Baka kudin dinkin...,
Nagode Nainah, Ya ajiye butar 聽da sauri
saboda kukan da naxo masa Shida Ya kamata
Ya ba yaransa amma yau suke bashi musamman
Nainah dake qarama acikinsu, yana sharar
kwallah Ya juya Nainah ta bisa da ido hr ya
shige masallaci kafin ta juya gidan
maqotansu......
0 Comments