MAGANIN SANYI NA MAZA

MAGANIN SANYI NA MAZA
Shi wannan sanyin gaskiya yana da wahalar
jin magani. Domin kuwa wadancan abubuwan
da ka ambata a baya, mutane da yawa sun
jarraba kuma sun samu waraka da yardar
Allah.
Amma ga wasu nan ga jarraba:
1. Ka nemi Man Habbatus sauda dan Misra
ko Algeria ko Hemani. Ka gaurayashi da man
Tafarnuwa Original tare da Man Albabunaj.
Sannan ka rika dafa 'danyar chitta (Ginger)
da ruwa kofi guda. idan ya dafu sai ka sanya
wancan Man chokali guda aciki, sannan ka
sanya zuma daidai gwargwado, sannan
kasha.
In dai sanyi ne, kowanne iri ne in sha Allahu
zaka samu waraka.
Ka samu Furen Albabunaj (chamomile flower)
ka rika dafa cokali guda kana sha kullum da
safe. In sha Allah Wannan zai wanke maka
Qodarka da mafitsararka, Kuma zai magance
maka Matsalolin ciwon sanyi.
WALLAHU A'ALAM.

Post a Comment

0 Comments