YIN RAKA'A GUDA 2 BAYAN FITOWAR ALFIJIR

YIN RAKA'A GUDA 2 BAYAN FITOWAR ALFIJIR

DARASI NA FARKO

Yana daga cikin nafilolin Manzon Allah ﷺ na yau da Kullum wanda yake yinsu kowane rana koda yana halin bulaguro,*Yin Raka'a biyu bayan alfijir ya fito,kafin sallar Assuba*yin hakan sunnance mai karfi.

*FALALAR WANNAN NAFILA*

Wannan Nafila tana da falala mai girma wanda Manzon Allah ﷺ ya bayyana falalarta da bakinsa da kuma aikinsa.

*Yin Raka'a biyu bayan fitowar alfijir yafi duniya da abinda yake cikinta falala da alkhairi*

Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
*(Yin Raka'a guda biyu bayan fitowar alfijir na nafila,yafi Alkhairin duniya da abinda yake cikinta)*

@رواه مسلم.

*Babu wata nafila da Manzon Allah ﷺ yake tsananta kiyayeta kamar Raka'a guda biyu bayan fitowar Alfijir*

Daga Umar Masu Imani Mai gaskiya yar Mai Gaskiya shugaban Matan masu Ilimi baki daya wato,Nana A'isha رضي الله عنه tana cewa;
*"Manzon Allah ﷺ babu wata nafila da yake tsananta kiyayewa kamar raka'a guda biyu bayan fitowar alfijir"*.
@رواه مسلم والبخاري.

*WANNAN NAFILA TA SAMU WASU ABUBUWA GUDA 5 MASU KEBANTATTU MASU MUHIMMANCI FIYE DA SAURAN NAFILOLI*

الشيخ محمد بن صالح العثيمين رحمه

الله؛-
Yana cewa;-
Wannan nafila ta bayan fitowar alfijir ta samu wasu abubuwa kebantattu kamar haka;-

NA FARKO
*An shar'anta yinta alokacin bulaguro da lokacin zaman gida*

NA BIYU
*Ladarta yafi Alkhairin duniya da abinda yake cikinta awajan Allah*.

NA UKKU
*An sunnanta saukakata wajan karatu da sauran aiyukan sallah,ba'a tsawanta karatunta ko sujada da ruku'u,Amma da sharadin cikasa wajibin sallah da rukunnanta*

NA HUDU
*Ana son a karanta wadan nan surori bayan FATIHA acikinta*

Raka'a ta farko bayan FATIHA;-
*قُلْ يَاأَيُّهَا الْكَافِرُونَ*

Raka'a ta Biyu bayan FATIHA;-
*قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ*

KO KUMA;-

Raka'a ta farko bayan FATIHA;-
*قُولُوا آمَنَّا بِاللَّهِ*
@البقرة : 136.

Raka'a ta Biyu bayan FATIHA;-
*قُلْ يَاأَهْلَ الْكِتَابِ تَعَالَوْا إِلَى كَلِمَةٍ سَوَاءٍ بَيْنَنَا*
@آل عمران: 52.

NA HUDU
*Ana ramata idan ta wuce ga wanda ya makara*.

@الشرح الممتع (4-71).



HUKUNCIN WANNAN NAFILA



Allah ne mafi sani

MU HADU A DARASI NA GABA INSHA ALLAH.

Post a Comment

0 Comments