Illa daya da Shinkafa ta kunsa Ga
Lafiyar Dan Adam
(shafinhausa)
Kasancewar Shinkafa ta zamto gama-gari a
fadin duniya, domin kuwa abu ne mai
wuya a rasata a gidan Talaka da mai kudi
sakamakon yadda al'ummar duniya suka
kafa mata kahon zuka na ta'ammali da ita
kusan kowace rana zata hudo kai.
Wani sabon bincike da aka gudanar a
jami'ar Havard ta kasar Amurka ya
bayyana cewa, da yawan mutane masu
ta'ammali da shinkafa a koda yaushe
suna yiwa lafiyar jikin su barazana da
cutar ciwon suga da a turance ake kiran
ta type-2 diabetes.
*shafinhausa*
*
*
*Akwai wasu binciken kuma da aka
gudanar a kasashen Sin, Japan, Amurka
da Australia kan mutane 352, 000 da
basu dauke da cutar ta ciwon suga, inda
bayan an dora su kan ta'ammali da
shinkafa na tsawon shekaru 4 zuwa 22
cutar ta fara bayyana jikin su.
*
*
*Baya ga cutar ciwon suga, wani sabon
bincike da aka gudanar a shekarar da ta
gabata ya bayyana cewa, shinkafa tana
tattare da wani sunadarin Arsenic
wanda ke da nasaba da cutar daji wato
kansa.
#Jaridar shafinhausa#
kucigaba da kasancewa damu
0 Comments