🌭🌮🌯K2 KITCHEN
*KUNUN SEMOVITA 1*
*semovita
*Busasshen inibi
*lemon tsami
*Alewa TomTom
*madara
*sugar
*YANDA ZA AYI*
_Ki dora ruwa a wuta ki bare alewar tomtom ki saka a cikin ruwan idan ruwan ya tafasa alewar ta narke sai ki zuba busasshen inibikin ki a ruwan dama kin dama semovita dinki, sai ki zuba ruwan zafin a kan gasarar,amma zaki matsa lemon tsami kadan ki zuba acikin ruwan gasarar Kafin ki dama, kisa sugar ki zuba madara ruwa ko ki dama ta gari ki zuba, yana da dadi sosai_
*WAINAR SEMOVITA*
*semovita
*yis
*koren tattasai
*bakar hota
*albasa
*attaruhu
*kwai
*mai
*YANDA ZA AYI*
_ki kwaba semovita dinki da ruwan da kika jika yis, kauri kwabin kamar na wainar shikafa,ki sa bakar hota kadan,ki rufi ki sa a rana ta hau sosai, ki yanka albasa da yawa ki zuba ki yanka Korean tattasai ki zuba ki jajjaga attaruhun ki zuba ki fasa kwai ki zuba kisaka sugar ki juya sosai, ki zuba mai a abin yin waina soyawa kamar yadda ake soya waina shinkafa._
*MIYAR AGUSHI*
*Agushi
*alaiyahu
*albasa
*kayan miya
*kayan kanshi
*dankalin turawa
*maggi
*curry
*YANDA ZA AYI*
_ki dafa dankalin ki ya dahu sosai sai ki aje a gefi kin jajjaga kayan miyar ki, ki soya su idan suka soyu sai ki sa ruwa kadan ki zuba agushin ki da dankalin da kika dafa Bayan kamar minti biyar sai ki zuba alaiyahun ki sai ki sauki zaki iya ci da wainar semovita da kukayi_
*Aci dadi lfy*
By Admins:
_Khadija Abubakar Umar(Maman Abdul)_
_Khdijah Yakub Ilu (Maman Sadeeq)_
0 Comments