*SOURCE DIN ZOGALE DA KWAI*
_KAYAN HADI_
*Taguru
*albasa
* zogale
* maggi
* citta
* mangyada
* gishiri
* curry
* kwai
_YADDA ZAKI HADA_
Ki jajjaga tarugu da albasa, tafarnuwa , ki wanke zolagale da ruwa ko da ruwan zafi ki yanka albasa akai. Ki dora tukunya a wuta kisa mai kadan ki yanka albasa ki soya saiki zuba jajjage idan ya soyu ki zuba zogalenki a ciki ki juya, kisa maggi da gishiri. Ki fasa kwai a roba kisa spices aciki ki kada kizu ba azogalen ki juya su hade saiki yita juyawa har ya tsane saikisa curry ki sauke. Ana ci da doya ko shinkafa anaci da couscous ko taliya da duk abunda kikeson ci da ita. Idan bakison kwai ba saikin saba kuma zaki iya data kwan ki yanka akai.
🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲
*HAUWAU YUSUF KGW*
07034321339
🌯Girki adon uwargida🌯1234
0 Comments