UQUBAR WANDA BAYA ZUWA SALLAR JUMA'A

_*UQUBAR WANDA BAYA ZUWA SALLAR JUMA'A*_

_Malamai sun kasa wanda baya zuwa juma'a zuwa kashi ukku:-_

_*1-Kashi na farko:* wanda baya halartar Sallar juma'a saboda wani larura ko uzuri kowani abu da shari'a ta dauke masa wajabcin juma'a kamar mata da kananan yara ko Matafiyi ko marar lafiya da dai sauransu._

_Wannan baya da laifi awajan Allah dan yana da uzirin akan rashin zuwansa juma'a._

_*2- Na Biyu:* Wadanda basu halartar Sallah juma'a suna masu inkari akan wajibcinta suna ganin ba dole bane zuwa Sallar juma'a wannan yana kaisu zuwa ga kafirci domin sun karyata Allah da Manzonsa kuma sun sabawa ijma'in malamai akan wajibcin Sallar Juma'a, wanda yake kan wannan mummunan fahimta hakika ya zama kafiri._

_*3- Na Uku:* Wanda baya zuwa sallar juma'a saboda kasala da ragwanci da wasa da addini amma yana mai kudurta Wajibine zuwa Sallar juma'a amma shaidhan ne yayi tasiri akansa. Me wannan hali ba'ace masa kafiri ana ce masa mumini mai raunin imani zamuso shi ta 6angaran Inda yake kyautata aiki mu kuma Qishi akan sabonsa, mai wannan hali da ire-iransa sune wandan nan Qububa take sauka akansu idan basu tuba ba._

_*UQUBAR WANDA BAYA ZUWA JUMA'A*_

_*1-Annabi ﷺ* yana cewa: *(Kudai wadansu mutane su hanu daga rashin zuwa Sallar juma'a ko kuma Allah yayi rufi akan zukatansu sai su kasance daga cikin Gafalallu)*_

*@ ﺻــﺤﻴﺢ ﻣــﺴﻠﻢ .*

_*2-Annabi ﷺ* yana cewa: *(Duk wanda yabar Sallar juma'a guda ukku da gangan batare da wani Uziriba, za'a rubuta shi cikin Munafukai)*_

*@ ﺻــﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ : ٦١٤٤*

_*3-Manzon Allah ﷺ* yana cewa: *(Duk wanda ya bar zuwa Sallar juma'a guda ukku ajere ba tare da uziri ba Allah zai dode zuciyarsa)*_
*@ ﺻـــــﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ : ٦١٤٣*

_*✍🏼Mustapha Musa*_

Post a Comment

0 Comments