WANDA YA KYAUTATA TARBIYYAR MATA UKU ZASU ZAMAN MASA HIJABI DAGA WUTA?

WANDA YA KYAUTATA TARBIYYAR MATA UKU
ZASU ZAMAN MASA HIJABI DAGA WUTA?

Amsa:
Hadisi yazo daga imamu Ahmad ya fitar masa da
sanadi ingantacce :
Daga ukubatu bin Amir yace : naji manzon Allah
s.a.w yana cewa:
(( Duk wanda ya kasance yana da yara mata
guda uku yayi hakuri dasu , kuma yaciyar dasu ,
kuma ya tufatar dasu , zasu kasan ce masa
hijabi da shiga wuta ranar alkiyamah. ))
FADAKARWA:
Wannan yana nuni akan falalar kyautatawa zuwa
ga yaranka mata kuma da tsayawa akansu da
al'amuransu . domin Allah ya kwadaitar damu
haka domin haka yana zama dalili na shigar
iyayen biyu aljannah da nisanta su daga wuta.
Allah yabamu wannan falala.

shafin hausa

Post a Comment

0 Comments