aslamu alaikum barkan mu da sake haduwa acikin wannan shiri Na filin girke girke,
to uwar gida sai gareki,
*YADDA AKE PAN CAKE DIN AYABA*
Akwai hanyoyi da dama na sarrafa ‘pan cake.’
Kowace mace na da irin nata yanayin sarrafa
girki, shi ya sa a kullum nake kara tunatar da mu
a kan cewa yana da kyau mace ta kasance mai
sarrafa sabon abu a kullum. Koda tuwo ne, yana
da kyau a kasance ana canja na’ukan miya domin
kara wa abinci armashi da kuma kin fita ran
masu ci.
A yau na kawo muku yadda ake sarrafa
‘pan cake’ din ayaba. A ci dadi lafiya.
*Abubuwan da za a bukata*
• Ayaba
• kwai biyu
• Madara
•Bata
• Sukari
• Fulawa
Hadi
A samu na’urar markada kayan miya (blender),
sannan a yayyanka ayabar a ciki. Bayan haka, sai
a fasa kwai biyu a ciki, sannan a zuba bata
(butter) kamar cokali uku zuwa hudu.
Daga nan
sai a zuba madarar ruwa ko a kwaba da madarar
gari da ruwa sannan a zuba. A zuba sukari da
garin fulawa kadan, sai a rufe na’urar a markada
su, har sai sun yi laushi sannan a sha.
A dora tukunya mara kama girki a wuta (non-
stick) bayan ta yi zafi, sai a rika debo kullun
ayaba ana zuba shi ta irin yanayin da ake so.
Idan ya dan nuna, sai a juya dayan gefen domin
shi ma ya gasu. Sannan a kwashe.
Za a iya cin wannan hadin da zuma ko da miya.
Wannan abincin an fi yin sa ne a matsayin
abincin karyawa.
*FILIN GIRKE GIRKE*
*WhatsApp* :08030727369 *Instagram*
:@girke_girke
*Twitter* :@girke_girke
*Facebook*: @girke.girke
By shafinhausa
0 Comments