Yadda ake Pepper Din Kayan ciki

Assalamu alaikum yan uwa barkan mu da kasancewa acikin wannan lokacin

Filin girke-girke

Na shafinhausa

Pepper Din Kayan ciki

Abun bukata

*Kayan ciki ko Nama
*Albasa
*Tattasai
*Attarigu
*Cabbage
*Ketchup(kadan)
*Kayan dandano
*Kayan kamshi

     -Yadda zakiyi

1, Ki wanke sai ki tafasa Kayan cikin, kizubar da Ruwan, ki sake dafa tumbin dan yafi su tauri karki manta da Kayan kamshi fa.

2, yanka Albasa(ring) da cabbage.

3, jajjaga Tattasai, Attarigu ki soyasu da mai Kadan .

4, kizuba Kayan cikin a soyayyen Tattasen nan

5, ki zuba cabbage din da Albasa

6, ki saka ketchup din Kadan ki jujjuya su. Shikenan sai ci

         
        Fateen

SHAFINHAUSA.TK

Post a Comment

0 Comments