YADDA AL’UMMAR MUSULMAI SUKA CAKUDA LAMARIN IMANI (2):
Kamar yadda muka Ambata a baya Al'ummar musulmai da dama sun cakuda lamarin IMANI ta fiskoki daban-daban,
To a wannan karon zamuyi magana akan yadda JAMA'A suka karkasu Wajen TABBATARDA IMANI. dakuma yadda kowa yake Taqaita IMANI akan Wani'abu abisa Jahilci da karkatar Zuciya.
IMAM IBNUL QAYYIM [Rh] -Kamar yadda yazo a Littafinshi AL’FAWÃ’ID- YACE:
Dayawa daga cikin Mutane Abinda suka dauka IMANI Shine kawai TABBATAR DA SAMUWAR MAHALICCI!
Wasu kuma IMANI a Wajensu shine FURTA KALMAR SHAHADA KAWAI!
Wasu kuma IMANI a Wajensu shine kawai MUTUM YA GASKATA CEWA ALLAH S.W.T SHINE MAHALICCIN SAMMAI DA KASSAI, KUMA ANNABI MUHAMMAD BAWANSA NE MANZONSA NE, KODA BAI TABBATAR DA HAKAN DA HARSHENSHI BA, KUMA KODA BAI AIKATA KOMAI BA!
Wasu Kuma IMANI a Wajensu shine INKARIN SIFFOFIN UBANGIJI S.W.T!
Wasu kuma IMANI a Wajensu shine BAUTAR ALLAH ABISA YADDA YAYI MASU ZAUQI/DA‘DI DA YADDA DUK SUKA GA DAMA!
Wasu kuma IMANI a Wajensu shine ABINDA SUKA SAMU IYAYENSU DA MAGABATANSU AKAI, Su asali ma sun Gina Imaninsune akan Shubhohi Guda biyu(2):
1-NA FARKO: Sai suce Ai wannan Abu da muke kanshi Shine Abinda magabatanmu da iyayenmu suke kai...”
2-NA BIYU: Sai suce: Kuma Abinda Magabatanmu suka fada ko suka aikata shine Gaskiya...”!
Wasu kuma IMANI a Wajensu shine kawai DABI'U NA KARAMCI DA KYAWUN MU’AMALA!
Wasu kuma IMANI a Wajensu shine kawai YIN WATSI DA DUNIYA DA ABUBUWAN DA SUKEDA ALAQA DA ITA!
مختصر الفوائد ص٤٢-٤٣
Bayan ya Ambaci Yadda Wadannan suka dauki IMANI sai yace:
وكل هؤلاء
لم يعرفوا حقيقة الإيمان، ولا قاموا به ولا قام بهم، وهم أنواع:
“Duk wadancan da aka Ambata a baya BASU SAN HAQIQANIN IMANI BA, Kuma basu Tsayu da IMANI ba shima IMANI bai Tsayu dasu ba (Imani yayi Gabas su Sunyi Yamma).
Kuma Wadannan Mutanen Nau'i Nau'i ne:
مختصر الفوائد ص٤٣
Sai ya Ambata mana Nau'ukan Wadannan Mutane kamar haka yace:
→×Daga Cikinsu Akwai Wanda yamayarda Abinda ke kishiyantar IMANI a Matsayin IMANIN!
→×Daga Cikinsu Akwai wanda yasanya Abinda Ba'a daukarshi cewa yana cikin IMANI a matsayin IMANIN!
→×Daga Cikinsu Akwai wanda yasanya Abinda yake Sharadi ne na samun Imani A Matsayin Shine IMANIN!
→×Daga Cikinsu Akwai wanda yasanya Abinda ke War-Ware IMANI da kishiyantarshi A matsayin Shine Sharadin Tabbatuwar IMANIN!
→×Daga Cikinsu Akwai wanda yasanya Abinda baya daga cikin IMANI ta kowace fiska a matsayin Shine Sharadin IMANIN!
A karshe sai Ibnul Qayyim yace:
والإيمان وراء ذلك كله،ووهو حقيقة مركبة من معرفة ما جاء به الرسول صلى الله عليه وسلم والتصديق به عقدا، والإقرار به نطقا، والإنقياد له محبة وخضوعا، والعمل به باطنا و ظاهرا، وتنفيذه والدعوة إليه بحسب الإمكان.
MA’ANA:
“Imani baya cikin dukan haka, Imani na haqiqa Shine IMANIN da aka Gina Akan Sanin Abinda Manzo s.a.w yazo Dashi da gaskatashi a Zuciya da Tabbatar Dashi a Furuci da miqa wuya gareshi cikin so da qanqan da kai, Da Aiki Dashi Zahiri da bad’ine, Da Aiqatar Dashi da kira zuwa gareshi Gwar-Gwadon iyawa...”!
📚مختصر الفوائد ص٤٣
والله تعالى أعلم.
✍by
shafin hausa
0 Comments