Bissimillahirrahamanirrahim
IDAN KINJI HAUSHI KIYI HAKURI!
Mace ba'a taba yi mata kishiya ta kirki.
1) In ka auro Ustaziya, tace: Munafukan gari, Allah
a baki, sharri a zuci, in ko ka auro 'yar gayu tace ta fitsare kafa, ba tada kamun kai.
2) In ka auro mai kyau tace kyalkyal banza, ka auro mara kyau tace an cuce ka.
3) In ka auro fara tace Sadaka Yalla ko Hasken Ambi, in baka ce tace Bayan Tukunya.
4) Ka auro daga danginta tace kana son bata zumunta, in kaje wani gun tace Tsintattar Mage.
5) Ka auro 'yar makota, tace wadda ta gama sanin sirrimmu?, in kaje nesa tace baa san asalinta ba.
6) In ka auro babba, tace an kwaso kwashi kwaraf, in ko karama tace girma ya fadi.
7) In ka auro kawarta, tace duk matan duniya?, don cin fuska da cin amana?, in ko ka auri 'yar aikin gidan, tace Tir !, wai iyakar wulakanci ke nan, kuma baka da taste.
8) Ka auro 'yar manya tace: Kuda wajen kwadayi akan mutu, in 'yar talakawa ka auro tace: Allazi Wahidin, Allah baku mu samu.
9) In ka auri 'yar amininka tace: Tsohon Banza, yau Baba ya koma Bobo, in ko abokiyar aikinka a ofis ka auro, sai tace: Abin boye ya fito fili.
10) In ka auro mai abin hannunta, sai tace: Kano Jiddah ko 'yar Dubai, in ko ba mai sana'a bace, tace an kwaso cima zaune.
11) In ka auro 'yar malamai tace asirce ka aka yi ba yinka bane, in ko 'yar bata da karatu, sai tace gidansu ko sallah baa iya ba.
12) In ka auro daga danginka, tace ana son a hade kai a ware ta, in kuwa bazawara ka auro, sai tace: In kaga godiya da sirdi, to wani ta kayar kuma wani mai gigi zata sake kayarwa..........
Yaushe kenan zaa auro kishiya ta kirki?
WAI MATA ME YA SA BA KU SON KISHIYA NE?
0 Comments