Bissimallahirahamanirrahim
Allahumma salli wasallim ala nabiyyin muhammadin,
posting daga shafinhausa
*ZUNUBAI GUDA BAKWAI MASU HALLAKARWA*
*Tambaya :*
Mal. wadanne abubuwa ne guda 6 da annabi yace mu gujesu suna hallakar da dan adam
*Amsa :*
To dan'uwa abubuwan guda bakwai ne kamar yadda suka zo a hadisin Bukhari mai lamba: 6857 da kuma Muslim a lamba ta : 262, inda annabi s.a.w. yake cewa : ku guji abubuwa guda bakwai masu hallakarwa:
*1.* shirka da allah.
*2.*sihiri
*3.* kashe rai ba tare da hakki ba,
*4.* riba.
*5.*cin dukiyar maraya.
*6.* juya baya a wajan yaki.
*7.* yiwa mata katangaggu kazafi.
Allah ne mafi sani
*Amsawa:*✍🏻
*Jamilu Yusuf Zarewa*
5/3/2014
*ZAUREN***DARUL-ISLAM*
Shafin Hausa ya dauki nauyin kawo muku,
0 Comments