ADDU'AR MAGANCE MUSIFU

ADDU'AR MAGANCE MUSIBU.

BismilLah.

A zamanin Sahabbai watarana anyi gobara awani Qauye daga cikin Qauyukan Madeenah.

Daga jin labarin Gobarar sai duk Mutanen Qauyen suka tafi aguje domin su kashe wutar daga gidajensu. Duk sun tafi in banda wani mutum guda.

Da aka tambayeshi mai yasa ba zai taho ba?,  sai yace ai shi wuta ba zata ta'ba cin gidansa ba.

Da suka je suka samu nasarar kashe gobarar daga gidajensu sai suka ga lallai wutar nan bata ta'ba gidan wannan mutumin ba, amma ta cinye duk gidajen dake kusa da nasa.

Don haka sukayi mamaki sosai. Da suka dawo suka tambayeshi menene sirrin abun? Kuma ta yaya ya tabbatar cewa Wuta ba zata ci gidansa ba?.

Sai yace "Ai Manzon Allah (saww) ya sanar dani wata addu'a wacce idan ka fadeta Allah zai kiyayeka daga dukkan Musibu.

Ga addu'ar nan kamar haka :

"اللهم أنت ربي لا إله إلا أنت عليك توكلت وأنت رب العرش الكريم، ما شاء الله كان وما لم يشأ لم يكن ، لا حول ولا قوة إلا بالله العلي العظيم. أعلم أن الله على كل شيء قدير و أن الله قد أحاط بكل شيء علما، اللهم إني أعوذ بك من شر نفسي ومن شر كل دآبة أنت آخذ بناصيتها، إن ربي علي صراط مستقيم.

Allahumma anta Rabbee la ilaha illa anta 'Alaika Tawakkaltu wa anta Rabbul 'Arshil Kareem.

Ma sha Allahu kana, wama lam yasha' Lam yakun. A'alamu Annal Laha 'ala kulli shay'in Qadeerun wa annal Laha Qad ahaata bikulli shay'in ilman.

Allahumma innee A'uzu bika min sharri nafsee Wa min sharri kulli daabbatin anta Aakhizun Bi naasiyatiha. Inna Rabbee 'ala Siratin Mustaqeem. (Qafa 1 safe da yamma).

KUYI SHARING DIN WANNAN ADDU'AR DOMIN JAMA'A SU AMFANA BAKI DAYA.

ASUBA TAGARI!

Post a Comment

0 Comments