KYAUTATAWA IYAYE_

*_RAMADAN: KYAUTATAWA IYAYE_*

1) Kyautatawa iyaye yana daga cikin manya manyan ibadu da ake neman kusancin Allah dasu. Watarana wani bawan Allah yazo wurin Abdullahi Ibn Abbas R. yace masa yayi manyan laifuka ciki harda kisan kai, sai Abdullahi Ibn Abbas yace masa mahaifiyar ka tana da rai? sai yace a'a sai Abdullahi Ibn Abbas yace masa kaje kayita istigfari ana tsammanin Allah ya gafar maka. bayan ya fice sai Mujahid yace wa Abdullahi Ibn Abbas: ya dan baffan Manzon Allah miyasa ka tambayeshi idan mahaifiyar sa tana da rai? sai Abdullahi Ibn Abbas yace: ban san wani aiki nigari da yake kusantar da bawa ga Allah ba kamar kyautatawa mahaifiya.

2) Duk wani aikin nafila dazakayi cikin Ramadan kamar karatun al-Qura'ni da sallar dare da sadaka  da zikiri ba wanda yakai ladar kyautatawa iyaye. kyautatwa iyaye wajibine cikin manyan wajibai wanda Allah yayi ta maimaita muhimmancinsa cikin al-Qurani haka ma Annabi S.A.W cikin hadissai dayawa.

3) Gaskiya mai daci itace:  Duk wanda yayi shekara 20 da rayuwa a cikin mutanen Nigeria yana tare da mahaifansa biyu, yana da wahala wasu shekara 20 su sameshi yana tare dasu. Mafiyawan ‘yan Nigeira suna rasa daya daga cikin mahaifansu ko duka biyu kafin sukai shekara 40 a rayuwa, kadan suke wuce hakan.

4) kayi amfani  da wannan damar domin kyautatawa mahaifanka. Kafin kakai suger da madara a waje ka tabbata ka fara dasu kamar yadda Annabi S.A.W yace gameda sadaka “kafara da Mahaifiyarka sannan mahaifinka sannan…. Sannan…”[ Bukhari] koda mahaifanka sun fika arziki zasuji dadin kyauta daga gareka. Ka tuna damace ka samu kuma zata iya kubcewa koda yaushe. Zakaga albarka a rayuwarka idan kayi haka insha Allah. Idan kuma iyayen sun rasu sai ayitayi musu addu’a a cikin wannan watan mai albarka.

5) Idan baka samu abinda zaka basu ba to kada zafin azumi da zafin aljihu yasa kagaya musu bakar Magana. Ka sassauta musu ka tausaya musu. Kyautatamu su da tausaya musu yana ka wo albarka ga rayuwa duniya da lahira.

Allah yabamu ikon yiwa iyayen mu biyayya.

*_Rubutawar: ✍🏼_*
*_Sheikh Dr. Jabir Sani Maihula {Hafizahullah}._*

Daga: *_ZAUREN ADDIINU ANNASIHATU._*

Post a Comment

0 Comments