*SIRRIN ALQUR'ANI DA SUNNAH WAJEN
MAGANCE CUTUKAN:* *Sihiri,hassada,maita da
shafar aljanu* *FITOWA TA 02* ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ
ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ Godiya ta tabbata ga Allah mai karamci
da kyauta,wanda ya ƙagi halittu,yasamarsu
alokacin babusu,kuma yake juya lamuransu da
abinda zasu rayu akansa tunda farko,Maɗaukaki
mai kyautatawa. Mahaliccin mutane da
aljanu,wanda albarkarsa tayawaita harya saukar
da: *( ﺳﻨﻔﺮﻍ ﻟﻜﻢ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﺜﻘﻼﻥ(* (ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ 31 ) ga
bawansa. Tsira da aminci suƙara tabbata ga
fiyayyen halitta Annabi Muhammad da iyalansa
da sahabbansa da duk wanda yabi tafarkinsu
har zuwa ranar sakamako. *ALAMOMIN
SAMUWAR SIHIRI AJIKIN DAN ADAM* Munyi
bayanin nau'ukan sihiri (14),amma ba
sukenanba,idan hali yayi za'aji wasu cikin
wannan gaɓar. *1.*Canjawar halin soyayya
zuwa ƙiyayya cikin sauri. *2.*Yawan faɗa
tsakanin masoya. *3.*Rashin karbar hanzarin
juna. *4.*Girmama laifi komai ƙanƙantarsa.
*5.*Canjawar kamannin miji awajen matarsa ko
matar awajen mijinta(zaizamo mummuna komai
kyawunsa,zata zamo haka komai kyauwunta).
*6.*Wanda akayiwa sihiri zaiji bayison wani
aikin amfani ga ɗan uwansa(mace ko namiji).
*7.*Bayason xama tareda ɗan uwansa(mace ko
namiji). *8.*Ko soyayya mai tsanani(wacce
tawuce ƙima). *10.*Son saduwa(jima'i)Wanda
yawuce misali. *11.*Rashin son yin nisa daga
masoyi(ga wanda akayiwa sihiri). *12.*Son
kyautatawa wacce tawuce misali.
*13.*Makauniyar biyayya. *14.*Ganin motsin
abinda baya motsi ko tsewar abinda yake
motsi. *15.*Ganin ƙarami amatsayin
babba,babba amatsayin ƙarami. Zaiga komai a
kamarda batasaba,saɓanin yadda mutane suke
gani. *16.*Tirjiya,ƙauracewa mutane da
mantuwa mai tsanani. *17.*Harɗewar zance ko
zance da ba'a fahimta. *18.*Ganin abin tsoro
afili ko cikin barci *19.*Rashin son zama awaje
ɗaya. *20.*Rashin tabbata akan aiki ko sana'a
ɗaya. *21* Rashin son zuwa wajen aiki ko
sana'a. *22* Lalacewar kasuwanci,kora daga
wajen aiki batareda wani daliliba.
*23.*Tarwatsewar iyali ko guje musu batareda
wani daliliba. *24.*Tafiya zuwa inda baisaniba
ko barci awaje mai ƙazanta. Zamu chigaba
insha Allah. Mun tattaro bayanai daga:
*1*. ﺍﻟﺼﺎﺭﻡ ﺍﻟﺒﺘﺎﺭﻓﻲ ﺍﻟﺘﺼﺪﻱ ﻟﻠﺴﺤﺮﺓﺍﻻﺷﺮﺍﺭ
.*2* ﺍﺳﺮﺭ ﺍﻟﻘﺮﺍﻥ ﻓﻲ ﻋﻼﺝ ﺍﻟﺴﺤﺮﻭﺍﻟﺤﺴﺪﻭﻣﺲ ﺍﻟﺠﺎﻥ
.*3* ﺍﻟﻤﻨﻬﺞ ﺍﻟﻘﺮﺍﻥ ﻟﻠﻌﻼﺝ ﺍﻟﺴﺤﺮﻭﻣﺲ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻧﻲ
.*4* ﻭﻗﺎﻳﺔﺍﻻﻧﺴﺎﻥ ﻣﻦ ﺍﻟﺠﻦ ﻭﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ Muhaɗu a
fitowa ta gaba. Daga: *AN NASIHA ISLAMIC
MEDICINE CENTRE TAKAI,KANO* Don ƙarin
bayani atuntubemu a: +2348065575014 Ko
hanyar email.(islamicannasiha77@gmail.com
0 Comments