Fitaccen mai bada umarni a fina finan Hausa na
Kannywood, Aminu S Bono ya bayyana
damuwarsa da yadda ake yawan fito da manyan
jarumai mata a kusan kowanni Fim, inda ya
bayyana hakan a matsayin wata babbar kalubale.
Daraktan ya koka kan karancin sabbin jarumai
Mata, inda yace hakan ne ya sanya tsofaffin
jarumai irinsu, Jamila Nagudu, Fati Washa, Aisha
Tsamiya, Hadiza Gabon da sauransu yin kane
kane a masana’antar Kannywood.
Bono ya cigaba da cewa kamata ya yi a ce
tsofaffin jaruman sun koma fitowa a matsayin
iyaye saboda girma ya fara kamasu, amma
saboda karancin sabbin jini ya sa duk an bi an
raja’a akansu, sai dai yace sun fara kulla
kulalliyar yadda zasu yi musu juyin mulki da
sabbin taurari.
“A yanzu mun fara fito da sabbin jarumai Mata,
da suka hada da Zee Preety, Amal Umar, Bilkisu
Shema, Zulaihat Ibrahim, Maryam Yahaya da
sauransu, ta hanyar fito dasu a bidiyon wakoki da
ba na fim ba. Inji su
Da yake amsa tambayar ko rashin ganinsu
Jamila Nagudu a Fim zai kawo nakasu ga
amsuwar Fim, sai yace “Su ma kafin su zo, su
Fati Muhammad ne ke haskawa, kuma zuwan
nasu ya kawo musu cigaba”.
Ya cigaba da cewa yanzu an wuce lokacin da
mata masu zaman kansu ke shigowa Fim, don
kuwa a yanzu a cikin Mata goma da zasu yi
rajistan fara Fim, za’a iya samun bakwai daga
cikinsu masu digiri ne ko kuma suna cikin
karatun digirin.
0 Comments