IDAN KAWUCE ..... KAYI BABBAN RASHI

IDAN KAWUCE ..... KAYI BABBAN RASHI =======================

      KAMAR YADDA YAZOMANA.
> Watarana ​Annabi Musa Alaihissalam​ zaije ganawa da Allah Madaukakin Sarki sai ya gamu da shaidan la'anatullahi alaihi akan hanya. Sai shaidan yace dashi: "Idan ka isa domin ganawa da Allah, ka nemamin gafara mana a wajenSa".
.
Sai Annabi Musa Alaihissalam yayi gaba yaje yagama ganawa da Allah Madaukakin Sarki ammana bai isarda saqon shaidan la'anatullahi alaihi ba.
.
Sai Allah Madaukakin Sarki da KanSa yace ga Annabi Musa: "Ya musa, ka tuna da saqo, ka tuna da alqawari".
.
Sai Annabi Musa Alaihissalam yace: "Ya Ubangiji! Shaidan ya aikoni akan cewa na nema masa gafara a wajenKa.
.
Sai Ubangiji Ta'ala yace: "na yarda zan masa gafara, ammana da sharadin sai yaje kabarin Annabi Adam yayi masa wannan sujudar dayaqi yin lokacin da aka halittashi".
.
Annabi Musa Alaihissalam yadawo yafadawa shaidan saqon da'aka bashi xuwa gareshi.
.
Sai shaidan yafara ququni yana cewa: "Yana da rai ma banyi masa sujuda ba sai yanxu daya mutu zanwa gawarsa, sam ina hakan bazai yiyuba".
.
Bayan yagama ququnin nasa sai yace: "kamar yadda kayimin alfarma a wajen Ubangiji, nima zan fada maka sharruka guda uku domin ka kiyaye.
.
Don Allah Idan Ku karanta ku turawa wasu domin suma su karu kuma su amfana.
.
1. Ka kiyayi fushi, domin duk lokacin da kayi fushi, nine a xuciyarka, nine idanunka, nine a cikin jikinka, nine a bakinka, zaka fita daga kamanninka na mitanen kirki, zaka koma siffar kare, zaka iya fadar maganar da sai kadawo hayyacinka zakayi nadama alhali babu lokacin yinta. Don haka ka kiyayi fushi domin inada sharri a wajen.
.
2. Ka tuna dani a duk lokacin da musulmai da kafirai suke gwabza yaqi. Inada sharri anan, Sai nazo ina rayawa mutum cewa: "kana mutuwa wani zai aure matarka, yayanka zasu shiga kunci na maraici, Anan mutum na juyawa da niyyar zai gudu shikenan makomarsa wuta kaga nasamu karuwa kenan.
.
3. Duk ranarda namiji baligi da mace baliga suka ke6ance, zan zamto nine na ukunsu. Zan qawata soyayyar juna a xukatansu. Bazan barsuba harsai sun afka alfasha. Kayi hankali da wannan ma.
.
Malamai sunyi bayani cewa:
.
Wadannan abubuwa da shaidan yafadawa Annabi Musa Alaihissalam darasine kuma nasiha ce ga al'ummar duniya baki daya har xuwa ranar sakamako.
.
Don ALLAH katurawa Share/Copy 'Yan Uwa don su Amfana batare daka canza komai ba.
.
Ya Allah Ya Ubangijin Musa da Haruna da soyayyar dake tsakaninka da annabi Muhammad (s.a.w)
Ka samu cikin masu hadiye fushi, Kasa muna cikin masu samun babban rabo duniya da lahira......,,,

Daga yasir Umar Jega

Barka da warhaka

Post a Comment

0 Comments