*_ITTAKAFI DA HUKUNCE-HUKUNCEN SHI_*
Ma'anar ittakafi itace lazimtar masallaci da manufa ta ibada, ko kuma zama a masallaci da kudurin yin hakan a matsayin ibada ga Allah. Sabanin yanzu, inda irin wadannan wurare malamai sun jaza matan aure sa iya shiga su yi ittakfin su, tsofaffin mata kuwa akwai inda akan ware a masallatan juma'a don sallar mata, suna iya zuwa nan. Babu ittakafi akan yarinya budurwa a masallaci ko bazawara mai kuruciya a tare da ita.
*_Tsawon Lokacin Yin Ittikafi_*
Malamai sun yi sabani a kan muddar yin ittakafi malaman Malikiyya sun ce mafi karancinsa kwana daya, watau wuni daya da darensa, saboda kuwa sun sanya yin azumi sharadi ne daga cikin sharuddan ingancinsa. Wasu malaman Malikiyya sun ce mafi karancin ittikafi shi ne lahaza, misali da mutum zai shiga masallaci ya zauna yana kirdadon sallah tare haka ya yi niyyar ittikafi don neman kusanci ga Allah, wannan ya isar masa ittikafi saboda su ba su sharadanta yin azumi daga cikin sharadin ingancinsa ba.
Tsawon kwanakin ittikafi abisa maganarcin zance ba shi da iyaka, ba a gwargwaje shi ba. Musulmi ya iya shardanta wa kansa shiga ittikafi na tsawon shekara a rayuwarsa, ba zai yanke ittikafinsa ba sai a kwanakin da aka hana yin azumi. Amma wannan ga wanda ya sa azumi yana daga sharadin ingancinsa.
Amma jamhurun malamai sun karhanta yin ittakafi sama da kwanaki goma, a wasun su kuwa sun karhanta shi idan ya wuce fiye da wata daya.
*_Mustahabban Ittikafi_*
1. An so ga mai ittikafi ya yawaita nafilfili da karatun Alkur'ani da ambaton Allah (zikiri).
2. Ga wasun Malikiyya an so yawaita nazarin Hadisan Annabi (S.A.W) da litattafan Fikhu da Tafsiri.
3. Ana son mai ittakafi ya dauki tanadinsa tare da shi kamar tufafinsa abincinsa da sauran abin bukata kamar magani, wanda ba sai ya bukaci fitowa ba.
4. Ba a son yawan Magana ko hira ga mai ittakafi – ba laifi in sulhu zai yi ko wani horo da alheri ko hani ga mummunan aiki.
5. Ana son mutum ya zabi babban masallaci saboda saukin makewayi da taron jama'a salihai haka ana son mutum ya zabi goman karshe don gabatar da ittikafi shi.
6. Ana son mai ittikafi ya tsananta ibada a daren 'Lailatul kadri' idan ya ga inda zai bi wata sallah ta 'Lailatul kadri' wadda ba a tsayar da ita a inda yake ba ya iya fita ya bi wannan tsayuwar, daga baya ya komo.
*_Abubuwan Dake bata Ittikafi_*
1. Yin jima'i da rana ko da dare, koda a wajen masallaci ne.
2. Inzalin maniyyi alhalin ido biyu, sakamakon sumba ko shafa ko tsawon tunani, don wannan duk suna cikin hukuncin jima'i.
3. Cin abinci ko abin sha da rana.
4. Zuwan haila ko nifasi.
5. Canja ra'ayi ko niyya fita daga ittikafi.
6. Fita daga masallaci bada wani uzuri ba.
*_Hanzarin Da Ya Halastawa Mutum Fita Daga Masallacin Yayin Ittikafi_*
1. Hanzarin na dabi'a kamar fitsari da wanka da kashi da habo da juma'a inda yake, da sharadin in an idar da sallah ya koma kan ittikafinsa ba a hira a hanya.
2. Hanzari na tilas kamar fitowa don kashe gobara, ko kau da wani kamar makaho ko yara daga abkawa rijiya, ko tsamo wanda ya fada ruwa, wannan fita ba ta bata ittikafi.
*Ramuwar Ittikafi*
Wanda ya shiga ittikafi na tadawwu'i sanan ya yanke shi don wani uzuri, an so ya yi kara'insa a kowane lokaci ya sami yalwa.
Allah ya maimaita mana, ya karbi idadunmu.
Rubutawa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.
0 Comments