KARIN GASHI YAYI TSAYI SANNAN KUMA YAYI YAWA GAMI DA BAKI.

ABIN BUKATA
1. Kwai Danye.
2. Roba mai Kyau mai dan fadi

YADA ZAKIYI
Kisamu wannan kwan naki saiki dauko wannan
roba taki saki fasa wannan kwan saiki cire
kwaiduwar kwan ma'an wannan yallon abin na
ciki ki ajiye gefe daya.

Saiki juye farin ruwan kwan a wannan roba
taki.

Idan gashin naki da dan yawa saiki fasa
kwan kamar uku-kodai yada yasamu.
Saiki dinga diban wannan farin ruwan kwan
kina shafeshi a gashin naki, har saikin
tabbatar cewa ruwan kwan ya ratsa ko ina
cikin gashin naki.
Saiki barshi tsawon mintuna 20 ko 30 saiki
wanke kan naki da sabulu mai kyau kina iya
amfani da sabulun Allo berra.

Kada kimanta cewa gashi yakan sanya mazaje
kara kaunar matayensu.

ALLAH ya temaka.

Post a Comment

0 Comments