Kudin SO Darasi NA Farko

Shirin zai rinka kawo tunani kala kala
acikin soyayya wanda masana na
musamman suka tattake guri akansa.

Zai shiryar da mutane akan soyayyya ta
gari.

Zai gyara tunanin mu akan haska ma
tubalen gina gamsasshiyar soyayya.
Shirin zai ameeentar da rayuwar kowanne,
mai bibiyarsa akan sanin sirrikan gina
soyayya tare da sirrikan cimma burin
soyayya zuwa aure..

Shrin zai daidaita sahun masoya akan
turbar nasara acikin mu amalar soyayya.
Shirin zai hakaito labarai dadada, na
masoya da tarihin gwagwarmayar soyayya
daga masoyan mu na baya…kamar
GIMBIYA FATRAH..

Sarauniyar kasar masar {misrah},wadda
tayi abun bajinta aduniyar masoya wadda
harduniya tatashi baza,amanta da itaba,

GIMBIYA DIYANAH

LAILA AL MAJNUN

SAHIBUL HUBBIN

YAREEMA QAMFAR

MASANI HUKKASH

MATASHI DAUDANUL FIKRAH

Dasauran ire irensu,,duka zamu haskasu
amadubin ilimi da nazari.. badon musha
labariba a’a don muma mu dauki
mahimman sakonni daga cikin labaransu,,
san nan shirin zai fede tsantsan ilimin
soyayya akan sananin…

MENENE MA SO ?

MENENE SOYAYYYA?

BABBANCIN SO DA SOYAYYA..?

SO YA KASU KASO NAWA.?

SOYAYYA TA KASU KASO NAWA?.

MENENE KAUNA..?

YA AKE SAMUN KAUNA..?

GINSHIKAN GINA SOYAYYA.?

MAHIMMANCIN YIN SOYAYYA..?

DABI,UN SOYAYYA..?

TASWIRAR SOYAYYA.?

KO KASAN TASIRIN WADAN NAN ACIKIN

SOYAYYA KUWA..?

KYAWU ?

HALAYYA ?

SHA,AWA ?

DUKIYA ?

NASABA ?

Duka wan nan shiri namu na KUNDIN
MASOYA zaiyi sukuwar Salla akan wadan
nan kyauwawan kalmomi nasama kafdinsu.

Shirinzai faifafye mana su afaifan nazari
don mukwashi ilimin sanin sirrin soyayya
azahirance…

MAQA SUDI…

Dalilin kirkiro wan nan shiri shine duba bisa
la,akari da abubuwa birjik wadanda soyayya
ta riga ta ratsa ta cikinsu, kusan dukkan
wani al,amari na rayuwa wanda ,dan Adam
yake walankeluwa acikinsa soyayya tanada
kaso sama da saba,in acikinsa..

Nasan zaku yarda dani idan nace maku.
Ita kanta wan nan rayuwar tamu tana bisa
doron soyayya ne tsakanin mu da uban
gijin mu, tsakanin mu da annabin mu,
tsakanin mu da manyan bayin Allah nagari,
tsakanin mu da iyayen mu, tsakanin mu da
yan uwan mu, tsanin mu da abokanan mu,
tsakanin mu da yammatan mu, tsanain mu
da sauran abubuwa, birjik na rayuwa…
To kenan taya kuke tsammanin za arayu
babu soyayya kodaya atsananin wasu
al,ummu..?

Duk da shirin namu zaifi karkata akalarsa
ne akan SOYAYYAR ZAMANI soyayya
datake tsakanin yammata da samari wadda
zatakai ga auratayya..ammazamu tabo
duka bangarorin…insha Allah..
GAREKU
Wan nan shiri ba nawa bane ni kadai..a a
hadin gwiwa ne tare daku,,kada kubarbi
nikadai inata zuba surutu kamar KURMAN
DAYA WARKE…

kuma kuzo mu tattauna ku sanyo
ra,ayoyinku da tunaninku.

Muyi hira muyi
muhawara inta kama.

Don dai duka mukaru da baiwar da Allah ya
hore mana,,,

DOGARO
wan nan shiri dazan fara gabatarwa ayau,
kaf dinsa kirkira ne da nazari da zurfafa
tunani da yawan bincike, kuma nike
tsarashi da shiryawa don kawai in nishadan
tar daku in fadakar da ilmantarwa kamar
yanda manufar wan nan gida namu take…
duk inkunga wani kuskure da laifi duka
daga ni yake ..ba daga kowaba sai ku
gafartar…

HASKE
zamu haska shirin ne bisa madubai guda
biyu rak, MADUBIN TAUHIDI MADUBIN
ZAMANI zamu kalli abun amahangar addini
da mahangar zamani.insha Allah..

Amma kada ace bamuyi komai ba awan
nan makon sai gabatarwa,,,bara muyi
tarayya daku acikin amsa wan nan
tambayar…

MENENE TUNANINKU GAME DA
SOYAYYA..?

Kowa yakawo ra,ayinsa kawai da iya
fahimtarsa tabbas zamu karu da juna…
kada kuraina wan nan yunkurin insha
Allahu zai zama mai dan Karen fa,ida ta
tasiri wata rana.

Muhadu a darasi nagaba

Post a Comment

0 Comments