Assalamun alaikum ya sahibul kalam
wahubbuz zaman, barkanku da war haka da
sake saduwa dani awani sabon shiri na
KUNDIN MASOYA,
Shiri na musamman wanda ke duba
aharkan SO da SOYAYYA acikin rigunan
MASOYA,
Gyara tare da tsaftace dukkan
zukata da suka shimfidu amanyan tarkunan
yammatan zamani, ko na samari yan bana
bakwai ,masu hada mak’atar sagale zuciyar
kowacce irin yar budurwa, wadda takai
matuka aduniyar cancara ado, tare da
walwalar SOYAYYA.
Idan kuna biye damu, awancan satin
nafara gabatar da sunayen kungiyoyin
masoya na duniya wadanda suka hadu
ataron masoya na duniya don kokarin fidda
sahihiyar ma,anar kalmar SO, wadda zata
zama karbabba aduniyar masoya kaf.
Don kokakri kaucema yawan fassara
ma,anar kalmar so da yawancink kowa
kanyi, alokacinda zuciyarsa ta ruwaita
masa kamar dai yanda na bayyana asatin
daya gabata.
Don haka ayanzu zan dorane daga inda na
tsara,
SAHIHIYAR MA’ANAR KALMAR SO
Bayan dukkan kungiyoyin masoya sun
gama halartar babban hotel dain masoya
na kasar sweetland.
Sai aka gabatar da babbar ajandar taro
wato fidda cikakkiya kuma sahihiyar
ma,anar kalmar so,bisa dogaro da nafsi
nafsi na manyan masana da suka hallara
awurin taron,
tabbas ayi musayar yawu da ra,ayoyi daga
bakunan mahalarta taron wadanda suka
dinga gabatar da ra,ayoyin su akan
kalamar ta SO bisa kafa hujja da bibiyar
tasniyyar ilimin so wanda kan iya tasori
azukata da hanyar shirya kwarewa da
nazari mai hasken fa,ida.
Bayan kwashe kanaki biyu ana ta kai ruwa
rana da tafka muhawara akan teburin
sanya so da soyayya na masana, sunkai ga
matsaya guda daya, wadda tazama
sahihiya ta fuskar yaddar masanan,
masanan sunyi duba daga farkon tsiron SO
da yake tufka azukata, da zuwa yaduwarsa,
ga sauran sinadaran sasssan jiki,kamar
jini,jijiya,da sauran sinadaran jikin dan
adam,
sai suka yarda kan cewa lallai, so zai iya
zama atsakankanin wasu mahimman
kalmomi kwaya biyu kacal,sune,
SWEET AND DANGER
SWEET,
Kamar yanda masanan suka bayyana
sweet shine tushen tsirar da ainifin kalmar
so azuciya, da kaso mafi tsoka na tunanin
samar da walwala da wanzajjen jindadi
aduk wata soyayya da ake da sherin
kullawa koma aka kulla,
babu shakka JINDADI, yana gaba gaba
asahun farko na limaman so da dashe mafi
tasirin fitowa azuciyar duk wanda akaso
ashukar mada soyayya, mai dan karen
tasiri.
Mafiya yawa nadaga jin sin samari da
yammata sukan fatsama acikin tekunan so
da soyayya ne kusan don samun walwalar
zuciya da nishadin rayuwa da jindadin
zaman takewa,
don haka masana sanin sirrin soyayya wato
msss suka tabbatar da kalmat sweet wato
jindadi amatsayin kalmar tazata fara amsar
bakuncin cikakkiyar ma,anar kalmar SO.
DANGER
Wan nan wata kalmace wadda akulli
yaumin tana nan tare da rayuwa basa
rabuwa, danger ko kuma atakaice muce
matsala, ko hadarin rayuwa ko rashin
jindadi, wani abune shima da zai zama
sananne atsakankanin SO da SOYAYYA,
Masana sun tabbatar da kamar yanda so
kan haifar da walwala da jin dadi azukatan
ma,abotansa haka yakan sadaukar da
bacin rai da kuncin zuciya da matsalar
rayuwa mai biye da kushen cimma burin
masoya ko wani bangarensu,
bisa dogaro da wadan nan bayanan ya sa
wancan taron masoyan suka kaikaita
akalarsu akan yin sukuwa da bibiyar wan
nan kalma ta so da bata ma,anar wadan
can kalmomon guda biyu,
sweet and danger
ma,ana,
JINDADI DA WAHALA
Sun hakikance cewa, duk wani masoyi
aduniya dayakama babbar turbar kulla wata
soyayya wadda tasamo asali daga so
dolene wadan nan yan tagwayen kalmomin
su halarci duniyar soyayyar mutum, kuma
suzama yan gaban goshi a dukkan tafiyar
soyayyar,
domin ba asamun soyayya mai tasirin
zama dukkanta jindadine zalla babu sabani
ko musgunawa ko kadan acikinta, dole wan
nan shine turba kuma al,ada ta so da
soyayya,
yau aji dadi gobe asha dankaren wahala,
wan nan shine hanyar so mikakka wadda
duk wani ruhi daya dandani zumar so sai
ya dandana madacinta wata rana.
Sun tabbatar da cewa kowacce irin
soyayya tana garawane akan wadan nan
tubalen guda biyu ne wato jin dadi da
wahala,wan nan yasa suka bata wan nan
ma,ana cikakkiya kuma karbabbiya ga
kowa da kowa na duniyar masoya,
da ance ma
whats love?
Kawai kanka tsaye kace
its sweet and danger
sweet na nufin dukkan wani jindadi da so
zai iya samarwa ga masoya.
Danger kuma na nufin dukkan wani tasgaro
da matsaloli da wahalhalu da so ka iya
haifarwa ga masoya,
wan nan shine karshen abinda taron
masoyan duniya suka samar na ainihin
sahihiyar ma,anar kalmar so bisa hujjoji da
bayanai kamar yanda kuka jisu ayanzu.
Wan nan shine karshen darasin mu
nayau,..insha Allahu asati na sama zamu
fara shiga cikin shirin gadan gadan mun
kammala da shimfida ayau.
Don haka tambayar mu tayau akan wan
nan darasi itace.
Meye ra,ayinku game da sahihancin
ma,anar so ta harshenka akan wan nan
ma,anar da masana suka fidda,?
ka yi fida mai ma,ana akanta.don musami
abin tattaunawa.
0 Comments