LABARI MAI BAN TAUSAYI......
Wata rana wani yaro dan shekara 10 yana
zaune
a wani bangare na Masallaci tareda wata
kanwarsa Karama.
Yaron yana ta rokon Allah Ta'ala babu
kakkautawa . Mutane suna ta wucewa babu
wanda ya lura da yaron balle ma yasan dashi a
wajen.
Sai wani Mutum bako yazo wucewa ya lura da
wannan yaron wanda yake sanye da wassu
matattun sutura a jikinshi amma kuma a wanke
suke fes. Mutumin ya lura duk fuskar yaron ta
yi
ca6a-ca6a da kwalla.
Har yazo kusada yaron yaron bai lura dashi ba
domin ya shagaltu da rokon Allah Ta'ala.
Mutumin sai yakama hannun yaron ya ce dashi:
"yaro menene kake nema haka a wajen Allah?".
Sai yaron yadaga kai ya kalli mutumin yace
dashi: "Mahaifina baya duniya, ina rokamar
Aljannah awajen Allah ne. Rashin mahaifin
nawa
ya kan sanya mahaifiyata kuka a Kullum, shine
itama nake roqon Allah Ya bata hakurin rashin
nasa.
Kullum kuma wannan kanwar tawa tana kukan
rashin sutura, itama ina rokon Allah Ya bani
kudi
domin na dauki dawainiyarta.
Sai mutumin ya tambayi yaron: "kana zuwa
makaranta kuwa"?
Sai yaron yace: "eh"
Sai mutumin yace: "a wane aji kake karatun?"
Sai yaron yace: "bana zuwa makaranta domin
karatu, sai dai kawai ina zuwane domin yin
talle.
Mahaifiyata takan yi Awara sai nakai
makarantar, yara da dama sukan saya daga
wajena idan nakai, kuma ta hakan muke samu
mu samu abun rufawa kanmu asiri"
Mutuminnan sai jikinshi duk ya mace kamar an
zubamar ruwan Sanyi. Sai yace wa yaron:
"bakuda wassu dangi ne a garinnan?
Sai yaron yace: "Mamana takan fadamin cewa:
talaka bashida dangi".muddin bakada kudi
aduniyannan to Kai marayane Koda kuwa
kanada iyaye balle Kuma ace sun rasu! Mamana
takasance ko
yaushe bata mana karya gaskiya takan fada
mana. Amman wani lokacin idan tasa mana
abinci nida Kanwata sai muce mata muci tare
sai tace mana tagama cin nata kafin mudawo
gida. A wannan wajen ne kawai nakan ga bata
fada mini gaskiya domin nasan bata ciba domin
kawai mu koshi take fadan haka".
Sai mutumin yace: "Idan wani ya dauki nauyin
karatunka zakayi?"
Sai yaro yace: "ai hakan ba zai ta6a yiyuwa ba,
domin yawancin yan Boko sun tsani talakawa.
Babu
wani Dan Boko daya da yadamu da yayi mana
magana balle kuma ace ya taimaka mana.
Dukkannin mutanen wajennan da kake gani sun
san mahaifina amma sam basuson su Nuna sun
sanmu".
Yaron yana kuka ya kara gayawa wannan
mutumin cewa: "uncle lokacin da mahaifina ya
mutu duk wadanda na sani sun dauke mu
kamar
wadanda basu sani ba, tamkar mu wasu
baqi ne".
Mutumin nan take shima ya fara zubar da
kwalla.
Da wannan nake Kira GA al_ummar annabi da
mudinga taimakawa Yan uwanmu marayu
sabida idon muka rasu muka bar "ya" yanmu
bamusan WA zai taimakamusuba. ALLAH
yataimakemu duniya da lahira.
0 Comments