Mata suna da matsaloli dayawa wanda yake
kawo masu rabuwar aurensu, daga cikin
matsalolin ga wasu kamar haka:
A -Kwadayi
B -Rashin biyayya
C -Rashin godiya
D -Rashin kula da dukiyar miji
E -Gasa
F -Daukar shawarar banza
G -Wulakanci
1-KWADAYI
Da yawa daga cikin mata sukan auri mutum
don kwadayin wani abu dake hannusa ko kuma
ya mallaka ko zato/saran ya mallaka, wannan
abun shine dalilin dayasa sukayi aure, bayan
anyi aure sunje gidan mijin, zasu tsaya su
tabbatarda cewa wannan abun da sukeso suna
samunshi, idan kuma yazama basu samu, to
zasu tada hankali akan cewa sai an sakesu,
wasu kuwa koda suna samu to duk sanda
akace wannan abun babushi ko kuma ya kare
to haka suma zaman su dakai yakare domin
abinda yakawosu yakare.
2-RASHIN BIYAYYA
Babban abinda mace zatayi tazauna gidan miji
hankali kwance shine biyayya, ita kuma
biyayya ta kunshi abubuwa da yawa. na farko
mace tasani cewa ta shirya yin duk abinda
mijinta keson tayi matukar bai saba ba,
sannan kuma tabar duk abinda mijinta bayaso,
sannan kuma tayi tunani da kuma kula da
dukkan abinda tasan zaisa mijinta farin ciki.
Mata dayawa basu da biyayya wanda shi kuma
namiji yake bukata, sakamakon haka dolene
aure ya rabu saboda rashin zaman lafiya.
3-KWALLIYA
Rashin iya kwalliya da kuma ado yana kawo
rabuwar aure, saboda shi namiji yanason yaga
matarsa cikin kwalliya a kowanne lokaci, zaka
samu cewa miji yakawo duk abinda ake bukata
na kwalliya amma ita kuma matar batayi, to
sai kaga yafi bukatar zama a waje fiye da
cikin gidansa domin sai matarsa tadaina
birgeshi, daganan sai yawan fada, sai kuma
rabuwa wanda wannan laifin matane.
4-ABINCI
Da yawa daga cikin mata ba’a koya masu girki
a gidajensu wanda sai sunyi aure sannan abun
ya zamar masu matsala, rashin iya girki
babbar matsalace a zaman aure wanda zaka
samu cewa duk abinda mace ta dafa babu
dadi ko kuma ba’a iyaci, shi kuma mai gidan
yana kawo duk abinda ake bukata wajen girki
amma babu biyan bukata wajen girki wanda
daga karshe idan yagaji sai kaga ya sakate
wanda wannan matsalar mace ce.
5-IYA MAGANA:
Wasu matan basusan yanda za suyi Magana
da mijinsu ba, sai kasamu cewa ga matar da
matukar kyau amma mijin baya gani saboda
rashin iya Magana, sai yaje waje ya biyewa
wadda batakai matarsa komai ba amma ta’iya
Magana, sai ta dauki hankalinsa wanda daga
karshe zaiji yagaji da ita wannan matar tashi
kuma saiya saketa ya kawo wata. Wannan
matsala ce ta mata.
6 -TSAFTA
Tsafta tana daga cikin abinda zaisa mijinki ya
soki, kamar tsaftar mahalli, da kuma yara,
namiji yanason yaga koda yaushe gidanshi da
kuma yaransa da tsafta amma wannan yayi
wahala a matan hausa/Fulani, wanda rashin
tsafta zaisa yagaji dake kuma ya tsane ta.
Cikin wani hadisi daga manzon Allah saw.yace
mana; Tsabta yana daga cikin Imini
(( Annazifatu minal Iman)) intaha".
7 -RASHIN GODIYA
Wasu matan na kasar hausa/Fulani basu da
godiyar akan irin kokarinda mijinsu yake masu,
kullum yana bakin kokarinsa amma basa gani
kuma basa godewa, wannan kuma yana kawo
matsala daga karshe daga karshe kaga anrabu
saboda yagaji.
8 -RASHIN KULA DA DUKIYAR MIJI:
Dukiyar miji tanada matukar mahimmanci
komin kankantarta, amma dayawa daga cikin
mata basa gani, sai subar dukiyar mijinsu ta
lalace suna gani wanda shi kuma mijin bayan
jin dadin haka, idan yayi iya kokarinshi bata
daina ba, karshe saiya saketa.
9 -SON GASA DA WASU
Wasu matan suna da gasar cewa duk abinda
akayi wa wata mace suma sai anyi masu
batare da kulawa da cewa mazajensu ba
karfinsu daya ba, zata matsama mijinta sai
yayi mata duk irin abinda tagani a wajen wata
macen wanda idan yagaji ko kuma bashi da
hali, to sai dai su rabu da ita.
10 -DAUKAR SHAWARWARIN BANZA
Wata macen bata da matsala da mijinta amma
tana daukar shawarar banza daga ‘yan uwa da
abokai, sukan bata shawarar banza akan
abinda zata yima mijinta ta cutar dashi ko
kuma ta hanyar sanya shi abinda baya iyawa
wanda idan dai baiyi suba sai dai ya saketa
11-WULAKANCI
Mata dayawa sukanso suringa wulakanta
mutanen da suka shafi bangaren mijinsu,
kamar iyayenshi, yan’uwanshi da kuma abokan
arzikinshi domin damar data samu ta zama
matar dansu, dan’uwansu ko abokinsu wanda
wasu mazan basa yarda da wannan to idan
har macen bata daina ba to sai su saketa,
12-MATSALAR AURE, BANAGAREN IYAYE
Iyaye suna da matsala wadda daga karshe
suke mayarda diyarsu jawara, su kuma
wannan matsalolin sune kamar haka:
• Auren Dole
• Kwadayi
• Rashin bincike
13-AUREN DOLE
Iyaye suna haddasa matsala wadda daga
karshe take kawo saki wato itace matsalar
auren dole, wasu iyayen suna takurawa ga
yayansu kan cewa sai sunyi masu auren
zumunci ko sunaso ko basuso wanda yin
hakan yanada matsala sosai don zakaga cewa
babu zaman lafiya bayan anyi auren domin
basu son juna ko kuma daya bayaso to babu
zaman lafiya wanda akarshe dole sakinta zaiyi.
Sannan wani auren dolen kuma bana zumunci
bane amma saboda iyayen suna tare ko abokai
ne saisu hada ya’yansu aure akan basa so
kuma karshe dole zai saketa.
14-KWADAYI
Sannan na karshensu shine auren dole domin
kwadayin abin duniya, don ganin cewa wanda
zai aureta yanada abin duniya kuma suna
ganin idanta aureshi zata samu kuma suma su
samu, to sai suce dole saita aureshi wanda shi
kuma yasan dalilinda dayasa aka bashi ita, to
duk ranar da yagaji da ita kawai sakinta zaiyi
domin dama yasan bata sonshi.
15 -RASHIN BINCIKE
Wasu iyayen basa bincike akan wanda yake
neman diyarsu ko kuma diyarda dansu yake
nema, sai azo ayi neman aure har a daura
aure batare da cikakken bincike ba, sai bayan
anyi auren sannan asami babbar matsala
wanda dole zasu rabu ya sake ta.
DAGA KARSHE:
Bincike a kotunnan gargajiya ya nuna cewa
duka ana samun kowa da laifi amma wa’anda
sukafi laifi sune mata wanda suke da kashi
arba’in da hudu (44) cikin dari na laifin
mutuwar aure, su kuma maza suna da kashi
talatin da daya (31) na laifin mutuwar aure, su
kuma iyaye suna da kashi Ashirin da biyar (25)
na laifin mutuwar aure a kasar Hausa/Fulani.
0 Comments