Kamar yadda ba kowacce Mace Namiji ke so
ba haka zalika ba kowana Namiji Mace ke so
ba.
Akwai wasu siffofin nagari dake tattare da
Mijin da kowacce macce ke so:
1.Mijin dake son matarsa bayan aurensu
fiyeda yadda yake sonta a layi.
2.Miji mai kishin matarsa. Domin Annabi
Sallallahu alaihi wasallam yace: “duk wanda
baya kishin matarsa bazai shiga Aljannah
ba”.
3.Mijin da ya dauki aure a matsayin Ibadah,
ba wai abin wasa ba ko kuma abin jin dadin
rayuwa kawai ba.
4.Wanda ya dauki matarsa a matsayin
abokiyarsa, kanwarsa, almajirarsa, kuma
abokiyar shawararsa.
5.Shine wanda baya zagin matarsa, baya cin
mutuncinta, baya cin zalinta, baya ha’intarta
koda a bayan idonta ne
6.Shine wanda yake zaune da iyalinsa cikin
amana da gaskiya da kyautatawa ba cuta ba
cutarwa. Wanda idan ya fahimci halayen
matarsa, yake hakurin zama da ita tare da
kyautatawa domin neman rahamar Allah
Ta’ala.
7.Shine wanda idan zai yi magana da
matarsa, zai fadi gaskiya babu yaudara ko
karya acikin zancensa.
8.Shine wanda ya dauka a zuciyarsa cewa:
Iyayen matarsa, Iyayensa ne. ‘Yan uwanta
ma ‘yan uwansa ne, kuma dangin matarsa
danginsa ne.
9.Shine wanda yake daukar cewa farin cikin
matarsa shine farin cikinsa kuma matsalar
ta, itama tasa ce.
10.Shine wanda ke kokarin kiyaye sirrin
matarsa, kuma yake kokarin kare mata
mutuncinta koda a wajen ‘yan uwansa ne,
tare da hikima da fahimtarwa.
11.Shine wanda baya fifita matarsa akan
‘yan uwansa, kuma baya tauye mata
darajarta. Yana bawa kowanne gefe nasa
hakkin kamar yadda shari’ah ta tanadar.
12.Shine wanda ya tanadi ruwan afuwa da
hakuri a cikin zuciyarsa domin kashe wutar
tashin hankali da bacin rai a duk lokacin da
hakan ta faru tsakaninsa da matarsa.
13.Shine wanda a kullum yake kokarin
tarbiyyantar da iyalinsa akan rayuwar addinin
Islama ba rayuwa irin ta yahudu da nasara
ba.
14.Shine wanda yake zaune da matarsa
komai dadi komai wuya ba zai dena nuna
mata soyayya ba wai
don tafara yankwanewa ko kuma karfinta
yafara raguwa.
15.Shine wanda yake bawa matarsa yabo a
duk lokacin da tayi kwalliya ko kuma tayi
girki komai rashin dadinshi. Miji nagari baya
raki baya ihu don yaji abinci yayi yaji ko
gishiri yayi yawa. Sai dai yace: “uwargida
abincin nan yayi dadi iyaka, sai dai gishiri
yayi mana shisshigi a ciki”
Allah Yasa mazaje su gane,su sauke
hakkinsu na kulawa..Ameen
0 Comments