ANNURIN ZUCIYA

Haske kan bayyana a
dausayin zuciya a yayin
da duhu ke gaggawar
ficewa daga gare ta ba
tare da ba ta lokaci ba....
Kafin zuciya ta kafa tutar
samun nasarar cafke
ragamar son wanda take
so, za ka same ta ne
tsundum cikin duhu mai
tsanani sakamakon rashin
samun mai yayyafa mata
feshin sinadarin so a gonar
ruhi.... Ruhin dan-adam
yana kasancewa ne cikin
wani irin yanayi na
kwadayin samun mai kula
da shi a kowanne lokaci,
wannan dalilin ne ya sa
zuciya ke tsananin son
duk mai kyautata mata
da kuma kin duk mai
takura mata.....
Kasancewar zuciya ita ce
tubalin ruhi sannan kuma
na'urar dake kimtsa soye-
soyen ruhi, sannan kuma
ma'adanar sirri, tana
kasancewa ne a cikin wani
irin yanayi mai hasken
gaske da zarar ruhi ya
sami abin da yake
muradi.... Tsananin hasken
zuciya yana tasiri matuka
dan kuwa har fuska tana
iya bayyanawa da zarar
ka ga wadda ke cikin
shaukin so nan take za ka
iya ganewa... Duban
masoya : a lokacin da
masoya biyu suka
kasance tare akwai wani
irin satar kallo da masoya
ke aiwatarwa a
tsakaninsu, kallo ne mai
girgiza zuciya har sai
zuciya ta kakkabar da
duk wata damuwa da ta
makale a jikinta. Hakika
kallon yakan sanyaya
zuciya matukar
sanyayawa musamman
idan an cakuda kallon da
kalaman so masu gigita
wanda aka yi dominsa.... A
lokacin ne masoya za su ji
tamkar su kadai ne a
duniya saboda tsananin
farin ciki da ya dabaibaye
zuciyarsu, gami da
tsananin haske tamkar
farin zinare wanda aka
ajiye shi a hasken farin
wata.... Hasken zuciyar
masoya a irin wannan
yanayi wa ne hasken
walkiya, domin ita
walkiya haskawa daya
take yi ta bace, amma
zuciyar masoya kuwa
hasken zai kasance
zaunanne a ruhi tsawon
zamani. Mhm! Soyayya
hasken rayuwa, rashin
soyayya kuwa kuncin
rayuwa.... Shin wai ma a
rayuwa akwai abin da ya
fi soyayya dadi kuwa?
Amma fa soyayyar da
aka kafa gininta da
tubalin gaskiya ne kadai
hakan ke faruwa.... Amma
ka ga soyayyar da aka
gina ta da tubalin karya
kuwa sunanta rusasshiya,
sannan kuma ba ta haifar
da komai sai damuwa da
kunci da kuma shigar da
masu yin ta cikin halin
ha'ula'i. Hasken so na
gaskiya shi ne fitilar dake
haskaka zuciya, hasken
zuciya kuwa hasken
rayuwa ne.

Post a Comment

0 Comments