Masana sun ce akwai fa’ida kwarai mace ta girmi mijin ta na aure

Wannan karo kuma mun kawo maku wasu
amfani na ace namiji ya auri Macen da ta
girmi sa.

Ko da dai hakan wani abu ne da
ba a saba gani a irin wannan Yankunan
amma kuma sam ba aibu bane har a
addini.

Masana zaman aure da kiwon lafiya da
masu karantar halayya da dabi’a sun ce
akwai amfanin mace ta girmi mijin ta.
Daga cikin amfanin da ake fada dai
akwai:

1. Rashin yarinta da wasa da hankali
Idan har mutum yayi dace da mace da
ta grime sa, to ya huta da yarinta da
duk wani shirme a wajen zaman aure.

A lokacin da mace ta kai wasu shekaru
dai za a same ta duk ta ajiye kallabin
wasa da hankalin namiji.

2. Samun abokiyar shawara
Idan namiji ya samu mace mai shekaru
yayi dace da abokiyar shawarar sa a
rayuwa.

Dalili kuwa shi ne ta san
rayuwa saboda dadewar da tayi ana
gogawa da ita.

Wadanda su ka riki
matan su abin shawara kuwa su na
samun nasara a rayuwa.

3. Iya kwanciyar aure
Masana har wa yau sun nuna cewa
manyan mata sun fi sanin harkar
zaman daki da tarawa a aure. Manyan
mata sun kuma fi rashin kyashi. Dama
dai ana cewa mai son girki ya auri
budurwa amma kuma mai son
kwanciya sai ya nemi babbar mace.

Post a Comment

0 Comments