RARRASHI
>Hakika rarrashi yana daya daga cikin
abubuwan dake sanya soyayya tayi karko.
Musamman a lokacin da daya daga cikinsu yayi
fushi,idan budurwarka ce tayi fushi sakamakon
wani laifi da kayi mata.
Sai kai ka sakko OGAH ka bata hakuri ka
rarrashi zuciyarta,ka tabbata kayi amfani da
kalamai masu sanyaya zuciya,to ina mai
tabbatar maka ko minti 5 ba'a yi zata hakura
idan har tana sonka da gaske. Haka kema 'yar
uwa idan Honey dinki yayi fushi sakamakon
wani laifi da kika masa,to ba fushi ya kamata
kiyi ba kema. Sai kiyi kasa da tattausan lafazinki
kiyi amfani da zakakan kalamai masu sanyaya
zuciyar masoyi,ko shakka babu idan har yana
sonki da gaske to nan take zaki ga ya sakar
maki wani lallausan murmushi.
Amma idan shi ya hau,kema kika hau to wa zai
rarrashi wani?
Masoya sai mu kula da wannan.
0 Comments