Jami'an 'yan sandan Najeriya dake a
rundunar jihar Legas sun bayar da labarin
yadda suka samu nasarar cafke wata
hatsabibiyar yarinya mai suna Dorcas
Adilewa da ta da kitsa sace kanta tare da
karbar kudin fansa zaga wurin mahaifin ta
mai suna Raiwo Adilewa.
Ita dai Dorcas din, jami'an 'yan sanda
sun cewa wata kawar ta ce mai suna
Ifeoluwa itace ta bata mafaka a gidan
da take duk dai a cikin garin Legas din.
Yadda wata hatsabibiyar yarinya ta kitsa sace
kanta tare da karbar kudin fansa daga mahaifin
ta a Najeriya
NAIJ.com ta samu cewa 'yan sandan sun
ce sun shiga maganar ne tare da fara
binciken lamarin lokacin da mahaifin
nata ya kai masu karar cewa wasu sun
sace masa diya kuma har ma sun bukaci
ya biya su Naira dubu dari 6.
Sai dai bayan dogon bincike da 'jan
sandan suka yi sai suka gano ba haka
bane yarinyar itace ta kitsa sace kan ta
domin ta karbi kudin daga wurin
mahaifin nata.
Sai dai ita yarinyar tace ta yi hakan ne
domin ta samu ta biya kudin
makarantar ta da tace uban nata yaki
biya yace bai da kudi.
0 Comments