Zamanin sauyin sheka: Yan majalisar APC guda 37 sun sheke zuwa PDP

Wani rahoto da muka samu da dumi dumi
yanzun nan ya tabbatar da cewa akalla
yayan majalisar wakilan Najeriya su
Talatin da bakwai ne suka yi fatali da
jam’iyyar APC, suka rungumi jam’iyyar
PDP.

Daga cikin wadanda suka fice daga APC,
guda Talatin da biyu sun koma PDP,
yayin da wasu guda hudu suka koma
suka koma ADC, daga bisan aka samu
wani guda daya da ya bayyana sanar da
yin murabus daga APC, amma bai
bayyana inda ya dosa ba.

Majalisar wakilai
Sanannu daga cikin wadanda suka fice
sun hada da Sani Rano, Barry Mpigi, Ali
Madaki, Dickson Tackighir, Hassan
Saleh, Danburam Nuhu, Mark Gbilah,
Razak Antunwa, Ahmed Bichi,
Abdulsamad Dasuki da Zakari
Mohammed.

Sai dai NAIJ.com ta ruwaito ba’a ambaci
sunan Kaakakin majalisar wakilai
Yakubu Dogara da na mataimakinsa
Yusuf Lasun ba a cikin yan majalisun
da suka yi hannun riga da APC.

Source:- Hausa.naija.ng

Post a Comment

0 Comments