Dandalin Kannywood: Zainab Indomie ta dawo harkar fim bayan hutun shekaru 5

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa
a masana'antar Kannywood watau Zainab
Abdullahi da aka fi sani da Zainab Indomie
ta sanar da dawowar ta harkar fim gadan-
gadan bayan kusan hutun dole da ta dauka
na shekaru biyar.

Zainab din dai ta bayyana hakan ne a
shafin ta na dandalin sada zumunta na
Instagram inda kuma ta ce ta samu
tangarda a rayuwar ta ne biyo bayan
kaiwa makura da tayi tun a farkon
shekarun kuruciyar ta.

Dandalin Kannywood: Zainab Indomie ta fadi
dalilin dusashewar tauraruwar ta

NAIJ.com ta samu cewa jarumar dai ta
roki Allah ya yafe mata dukkan kura-
kuran da ta aikata a baya da wanda ta
sani da wanda ma bata sani ba domin a
cewar ta yanzu ta bude sabon shafi ne a
rayuwar ta.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a baya
jarumar tayi fice a masana'antar sosai
kuma a cikin kankanin lokaci wanda
hakan ne ma janyo mata dubban
masoya da kuma makiya da dama.

Post a Comment

0 Comments