Na hadu da 'yan Boko Haram a gidan yari kuma sun fada min su waye suka kirkiri kungiyarsu - Al-Mustapha


Na yafewa duk wadanda suka
gana min azaba ta tsawon
shekara 15 – Al-Mustapha


Major Hamza Al-Mustapha, tsohon dogarin
tsohon shugabn kasar Najeriya a mulkin
soji, marigay Janar Sani Abacha, ya
bayyana cewar ya yafewa dukkan masu
hannu cikin ukubar da aka shafe shekara
15 ana gana masa.

An kama tare da tsare Al-Mustapha ne
bisa zarginsa da kisan Kudirat Abiola,
uwargidan mutumin da ya lashe zaben
shugaban kasa na shekarar 1993,
marigayi Moshood Abiola.

Na yafewa duk wadanda suka gana min azaba
ta tsawon shekara 15 – Al-Mustapha
Da yake jawabi a wani taro na
kungiyoyin Kiristoci fiye da 40, Al-
Mustapha, ya bayyana cewar ya yafewa
kafatanin masu hannu a daurin da aka
yi masa.

A cewar Al-Mustapha, sau 11 ana
yunkurin hallaka shi a kan laifin da bai
san komai a kai ba amma Allah yana
kubutar da shi.

Sannan ya kara da cewar akwai wasu
muhimman bayanai da ya samu a kan
kungiyar Boko Haram lokacin da yake
gidan yari tare da bayyana cewar wasu
‘yan boko ne suka kirkiri kungiyar.

“Sun kawo ‘yan Boko Haram 138 dakin
da nake a gidan yari, bayanan da suka
sanar da ni ba zan iya fadawa ‘yan
Najeriya ba saboda dalilan tsaro” a
cewar Al-Mustapha.

Kazalika ya bayyana cewar an kirkiri
rikicin makiyaya da manoma dagan-gan
domin kawar da hankalin ‘yan Najeriya
daga wasu abubuwa dake faruwa a
kasa.

Sai dai bai bayyana ko wadanne
abubuwa ne ba.

Source @hausa.naija.ng

Post a Comment

0 Comments