Wani faifan bidiyo da yayi ta yawo a
kafafen sadarwar zamani da kuma ya
dauki hankalin jama'a da dama
musamman ma a arewacin Najeriya na
dauke ne da yadda wani soja ya nunawa
budurwar sa kauna a gaban jama'a a
jami'ar Kano.
Bidiyon dai ya nuna sojan sanye da
kakin sa da ake kyautata zaton soyayya
suke da budurwar ya durkusa a gaban
ta yana rokon ta amince da soyayyar sa.
Soyayya ruwan zuma: Yadda wasu masoya suka
kwashi 'yan kallo a jami'ar Bayero ta garin Kano
(Bidiyo)
NAIJ.com ta samu cewa saurayin a cikin
wani irin salo na koyi da turawa, ya
fiddo zobe daga aljihun sa inda ya
kuma bukaci budurwa da ta mika
hannun ta domin ya saka mata.
Sai dai budurwar wacce take a cikin
shiga ta hausawa sanye da doguwar riga
da kuma jan gyale ta fashe da kukan
murna ne inda ta ma kasa hada ido da
shi.
0 Comments