Mun ji cewa masu neman takarar kujerar
Shugaban kasa a karkashin Jam’iayyar
adawa ta PDP sun hadu jiya Talata da
yamma.
Yanzu haka PDP na shiryawa
zaben fitar da gwani da za ayi kwanan
nan.
Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido da
Tambuwal wajen taron PDP
Tsohon Mataimakin Shugaban kasa
Atiku Abubakar, Ahmad Makarfi da
kuma Shugaban Majalisa Bukola Saraki
da tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa
Kwankwasoda kuma Gwamnan Sokoto
Aminu Tambuwal su na wajen taron.
Haka kuma sauran ‘Yan takara irin su
tsohon Minista Kabiru Taminu Turaki
da tohon Shugaban Majalisar Dattawa
David Mark da tsohon Gwamnan Jigawa
Sule Lamido da sauran masu neman
Shugaban kasa irin su Datti Baba-
Ahmed.
Shugaban PDP na kasa watau Uche
Secondus ne ya jagoranci wannan zama
da aka yi.
An samu halartar wasu
Gwamnonin PDP irin su Gwamnan
Bayelsa Seriake Dickson; da kuma
Gwamnan Kwara Abdulfatah Ahmed da
Ayo Fayose.
Kamar yadda mu ka samu labari daga
Bukola Saraki an yi taron an tashi
lafiya.
Tsofaffin Gwamnoni irin su
Alhaji Attahiru Bafarawa da Jonah Jang
wadanda su na cikin masu neman
kujerar Shugaban kasa sun halarci
wannan zama.
Mun samu labari cewa wasu Magoya
bayan Buhari sun kashe wani Direba
har lahira bayan sun jefa sa lokacin da
ya tuko Tawagar tsohon Mataimakin
Shugaban kasa Atiku Abubakar zuwa
Kaduna.
0 Comments