Siyasar Kano: Rikicin mabiya
Shekarau da yan Kwankwasiyya
ya kai ga Masallacin Juma’a
A yayin da zabukan shekarar 2019 ke
cigaba da karatowa, farfajiyar siyasa na
cigaba da kazanta a sanadiyyar banbance
banbancen ra’ayi a tsakanin mabiya
akidun siyasa daban daban, musamman a
jahar Kano.
Wannan hasashe ya tabbata a jahar
Kano, inda mabiya siyasar Sanata Rabiu
Musa Kwankwaso da aka fi sani da yan
Kwankwasiyya da mabiya Malam
Ibrahim Shekarau suka yi fito na fito,
kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.
Majiyar NAIJ.com ta ruwaito wannan
lamari ya faru ne a ranar Lahadi, 16 ga
watan Satumba a yayin daurin aure
wani matashi mai suna Ali mai salati a
Masallacin Juma’a na Murtala dake
birnin Kano.
A yayin wannan fada data kaure
tsakanin yan kwankwasiyya da yan
Shekarau an jikkata wani matashin
Kwankwasiyya guda daya, mai suna
Amir Abullahi Kima, tare da tarwatsa
taron jama’a da suka halarci daurin
auren.
Sai dai wannan sabon tabarbarewar
dangantaka tsakanin magoya bayan
Kwankwaso da na Shekarau ya samo
asali ne tun bayan ficewar Malam
Ibrahim Shekarau daga jam’iyyar PDP,
inda ya fada APC bayan Rabiu
Kwankwaso ya shiga PDP.
A yanzu haka dai a iya cewa siyasar
jahar Kano ta sauya zani, musamman
ga yadda Shekarau ya yanki tikitin
tsayawa takarar Sanatan Kano ta
tsakiya, kujerar da Kwankwaso yayi
dare dare akai, Alhali a baya
Kwankwaso yayi zaton zai hada kai da
Shekarau su kada Ganduje.
0 Comments