Dandalin Kannywood: Ali Nuhu ya bayyana fim din yafi so a rayuwarsa

Shahararren tauraron harkar fina finan
Hausa, Kannywood, Ali Nuhu da ake yi ma
kirari da suna ‘Sarkin Kannywood’ ya
bayyana fim din dayafi burgeshi tun daga
farkon shigarsa harkar fim zuwa yanzu.

A sanadiyyar Fim din Mansoor, Ali
Nuhu ya lashe babbar kyauta a bikin
karrama yan Fim da fina finan yankin
Afirka da gidan talabijin na Afirka
Magic ta shirya mai taken ‘Africa Magic
Viewers Choice Award’ daya gudana a
ranar Asabar a jahar Legas.
Karramawar
Bugu da kari Fim din Mansoor wanda
aka yi shi akan labarin wani matashi da
aka haifeshi na ta kan hanyar aure ba,
kuma Ali Nuhu ya shirya kuma bada
uamrni, ya lashe kyautar Fim mafi
kayatarwa da aka shirya da harshen
Hausa.

Gidan rediyon bbc hausa ta ruwaito Ali
Nuhu yana bayyana cewa duk a cikin
fina finan da yayi, bai taba yin fim din
daya kai ‘Mansoor’ ba, sakamakon yayi
amfani da kayan kimiyya da kuma
kirkire kirkire da dama a cikinsa.

A cikin, Mahaifiyar Mansoor ta yi
kokarin boye masa daya shafi asalinsa,
amma fa daga bisani ya nemi sanin
gaskiyar halin dayake ciki sakamakon
soyayya data tunzura shi, bayan iyayen
yarinyar dayake so sun yi masa gori.
A jawabinsa ga majiyar NAIJ.com , Ali
Nuhu yace wannan irin zarra da
Mansoor yayi ya faranta masa,
sa’annan yace Mansoor ya samu
wannan nasara ce sakamakon anyi
amfani da fasahar kirkire kirkire da na
kimiyya a cikinsa, wanda ba’a taba
samu a waninsa ba a Kannywood.

Ali Nuhu ya bayyana jigon shirin
Mansoor a matsayin juriya da tawakkali
a yayin da mutum ya tsunduma cikin
mawuyacin hali, darasinda dake cikin
shirin kuwa shine “Duk abinda aka ga
ya samu mutum a rayuwa, kada ayi
masa gori” Inji shi.

Daga karshe Ali Nuhu ya kara da cewa
ya samu adadin kyautuka da lambobin
yabo da dama tun daya fara hakar fim
a basu taba kirguwa ba, duk da haka
yace zai cigaba da shirya fina finai
masu kayatarwa da ilimantarwa.

Post a Comment

0 Comments