Hadiza Gabon ta birge cikin kayan anko da tayi da diyar ta

Idan baku sani ba jarumar Kannywood Hadiza
Gabon tana da diya duk da cewa bata yi aure
ba.

Fitacciyar Jarumar masana'antar
Kannywood Hadiza Aliyu Gabon ta birge
tare da diyar Maryam a wannan hoton da
suka yi.

Tauraruwar fim ta wallafa hoton su tare sanye
da anko cike da fara'a a shafin ta na Instagram.

Idan akwai mai tunanin yadda rayuwa zata
kasance idan mutum ya haihu, ganin yadda
jarumar da diyar ta ke narkar da zukatan jama'a
duba da irin wasa da dariya da suke yi zai
taimaka wajen samun ansar farin cikin da
haihuwa ke haddasa.

Ga masu neman sani, jarumar bata yi aure ba
amma kuma tana da diya.

Hadiza Gabon ta karbi rainon Maryam Aliyu ne
shekarun baya kuma tun lokacin shakuwar su na
cigaba da kamari.

Ga masu bibiyan shafin ta na kafafen sadarwa,
mawuyaci ne jarumar ta wallafa wani sako ko
hoto a shafin ta ba tare da saka diyar ba.

Maryam ta zama tamkar jaruma ga wasu masu
bibiyan shafin Hadiza, da yawa sukan bukace ta
da ta isar da sakon gaisuwa ga diyar.

Hadiza Gabon tana son yin aure
Shahararriyar 'yar fim din Kannywood din nan,
Hadiza Gabon, ta ce tana so ta yi aure amma
lokaci ne kawai bai yi ba.

Da take hira da BBC, Hadiza ta ce aure lokaci
ne, kuma kamar mutuwa, idan Allah ya kawo shi
babu yadda mutum zai guje masa.
Hadiza Gabon, ta ce babu wacce za ta so ta
rinka kaiwa-tana-komowa a gaban iyayenta ba
tare da ta yi aure ba, alhalin kuma ta kai
munzalin yin hakan.

"Wallahi babu wata mace da za ta so ta kai lokacin
aure amma ta ki yi" inji Gabon.

Post a Comment

0 Comments