INEC Hukumar zabe zata haramta amfani da waya wurin zabe

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya
(INEC) ta haramta zuwa wurin kada kuri'a
da wayar salula.

Shugaban hukumar Farfesa Yakubu Mahmood
ya sanar da haka ranar litinin yayin da ya gana
da jama'a a garin Osogbo gabanin zaben jihar
Osun da za'a gudanar ranar asabar 22 ga watan
Satumba.

A labarin da Channels ta fitar shugaban
hukumar yace an dau matakin ne domin
magance matsalar magudin zabe.
Ya bayyana cewa za'a haramta masu zabe
amfani da waya da zaran an mika masu takardar
kada kuri'a.

Ana zargin cewa masu zabe na daukar hoton
takardar kada kuri'ar su ne domin tabbbatar ma
wakilan jam'iya wanda suka dangwala ma kuri'a.

A cewarsa, za su soma tabbatar da haramcin ne
a zaben da za a yi a jihar Osun da ke kudu
maso yammacin kasar ranar Asabar mai zuwa.
Hakazalika mai magana da yawun hukumar,
Mallam Aliyu Bello, ya tabbatar da wannan
labarin kamar yadda rahoton BBC ya bayyana.
Malam Aliyu ya ce bisa fahimtarsu, masu sayar
da kuri'unsu suna kulla yarjejeniya ta yadda
masu sayar da kuri'a za su nuna wa masu saye
wata shaida da za ta gamsar da su cewa
jam'iyyarsu mutum ya zaba gabanin su biya shi,
don haka wannan dokar za ta magance wannan
matsalar.

Jami'in na hukumar zabe ya yi kira ga 'yan kasar
da su ba su hadin kai wurin ganin sun aiwatar
da dokar ba tare da fuskantar matsaloli ba.

Post a Comment

0 Comments