- An dai maida talakawa sha-ka-tafi ne,
inda zaka ga gwamna da Sanata da Minista
suna musayar kujerunsu a jiha daya,
kamar babu wani wanda ke da iko ko
damar lekawa ciki.
- Tun daga 1999 har izuwa yanzu, kamar
dai har yanzu tsakaninsu suke musayar
kujeru
- Tsohon gwamnan ya Kwatanta rahoton da
karya, yace Kato bayan Kato kadai zai
tabbatar da hakan
Kujerun Sanata da gwamnoni sun fara hada fada
a jihohi, tsakanin gwamnoni da Sanatoci
Ban mikawa Geidam tikitin kujerar
sanatan Yobe ta yamma ba.
Zaben fidda
gwani na Kato bayan Kato kadai zai iya
ba wa mutum tikitin.
Wannan
damokaradiyya ce.
Tsohon gwamnan jihar Yobe, Sanata
Bukar Ibrahim, yace bai mika tikitin
kujerar Sanata ga Gwamna Ibrahim
Geidam ba. Ibrahim ya bayyana hakan
ne a lokacin da yake maida martanin
rahoton da aka bada ta yanar gizo,a
garin Damaturu.
Tsohon gwamnan ya Kwatanta rahoton
da karya, yace Kato bayan Kato kadai
zai tabbatar da hakan.
Yace damokaradiyya akeyi kuma ita
mukeyi a jam'iyyar mu ta APC. Mutane
ne zasu tantance, kuma suna da damar
zaben ra'ayin su.
An dai maida talakawa sha-ka-tafi ne,
inda zaka ga gwamna da Sanata da
Minista suna musayar kujerunsu a jiha
daya, kamar babu wani wanda ke da
iko ko damar lekawa fadar mulki.
Tun daga 1999 har izuwa yanzu, kamar
dai har yanzu tsakaninsu suke musayar
kujeru.
0 Comments