mike Ezurounye Jarumin Nollywood ya bada dalilin da yasa ya saka Hadiza Gabon a cikin shirin sa

Ta shaida cewa ta amince da fitowa cikin
shirin bisa ga ka’ida na cewa baza ta fito a
matsayin da zai sabawa addini ko al’adar ta.

A kwanan baya mun kawo maku labarin
cewa fitacciyar jarumar Kannywood ta fito
a cikin wani shirin fim na turanci wanda
shine na farko da zata yi aiki a
masana'antar fim na Nollywood.

Jaruma mai tauraro ta nuna farin ciki game da
wannan damar na yin fim da wasu jiga-jigan yan
wasan Nollywood.

Ta shaida ma BBChausa cewa ta amince da
fitowa cikin shirin bisa ga ka’ida na cewa baza
ta fito a matsayin da zai sabawa addini ko
al’adar ta.

Tana mai cewa;
“Fitaccen jarumin Nollywood Mike Ezuruonye ne
ya gayyace ni na fito a wani fim dinsa mai suna
'Lagos real fake life'
"Tun da ya gaya min cewa zai so na fito a fim
dinsa, na shaida masa cewa ba kowacce rawa zan
taka ba. Ba zan fito a matsayin da zai saba da
addini da al'adata ba"
Jarumar ta shaida cewa babu wani bambanci
tsakanin yadda ake yin fina-finai a kannywood
da nollywood face bambancin harshe.

Shahararren jarumi wanda ya shirya shirin yayi
karin haske game da dalilin saka jarumar cikin
shirin duk da cewa bata taba fitowa a cikin wani
shirin Nollywood.

Zantawa da muka yi dashi yayin da ya kawo
mana ziyara, Mike Ezurounye ya nuna
gamsuwar sa yin aiki da ita.

Yayin da yake bada amsar dalilin saka ta a
shirin, jarumin yana mai cewa "Ni mutum ne
wanda ke son saka abun mamaki a cikin fim.

Hadiza tana da basira, ta kware kuma bata taba
yin fim a Nollywood ba"
"Na ware lokaci na musamman domin inyi bincike
akan ayukan ta kuma na tambayi jama'a da dama
game da basirar ta" ya kara.

Mike yace Hadiza ta bada hadin kai dari-bisa
dari kamar yadda ya kamata kuma a bangaren
su sun kiyaye duk wani ka'ida da al'ada da
addininta ya tanadar.

A cewar shi ya ji dadin aiki da ita matuka kuma
akwai wasu aiki biyu da zai so ya kara saka ta
a ciki.

Daga karshe jarumin ya jinjina ma masana'antar
Kannywood, yace kofar shi a bude take wajen
yin aiki da masa'antar.

Shirin 'Lagos real fake life' tana fadarkar da
jama'a game da rayuwar karya da wasu suka sa
a ransu. Manyan fitattun Nijeriya daga
masana'antar fina-finai dake kasar suka fito a
ciki har ma da jaruman kasashen waje.

Za'a fara haska ta ga sinima cikin watan
Nuwamba.

Post a Comment

0 Comments