NEA 2018 Ali Nuhu ya sake fitowa takarar gwarzon shekara

'Sarkin Kannywood' ya fito takarar gwarzon
shekara tare da manyan fitattun jaruman
Nijeriya a rukunin jagoran shiri na gasar.

Bayan ya lashe lambar yabo ta gasar
AMVCA na bana » , fitaccen jarumin fina-
finan hausa Ali Nuhu ya sake fitowa takarar
gwarzon shekara na gasar Nigerian
Entertainment Awards.

'Sarkin Kannywood' ya fito takarar gwarzon
shekara tare da manyan fitattun jaruman
Nijeriya a rukunin jagoran shiri na gasar.

Zai fafata da jarumai, Femi Adebayo, Blossom
Chukwujekwu, Kalu Ikeagwu, Ali Nuhu, Adebayo
Salami da Odunlade Adekola wajen lashe
lambar yabo.



Ya fito takarar ne bisa rawar da ya taka a cikin
shirin 'Mansoor'.

Bikin Nigerian Entertainment awards tana daya
daga cikin manyan bukukuwan karrama fitattun
jarumi da suka nuna hazaka a dandalin nishadi
ta kasa baki daya.

Ta sha bambam da sauran
domin ana gudanar da bikin ne a wajen Nijeriya.

Bikin na wannan shekarar shine na 13 kuma za'a
gudanar da ita ne a birnin Washington DC na
kasar Amurka ranar 10 ga watan Nuwamba.

Ga sauran jaruman da suka fito takara a gasar
bana kamar haka;
Ali Nuhu ya lashe kyautar AMVCA
Gasar African Magic Viewers Choice Awards
wanda aka shirya a birnin Legas ranar asabar 1
ga watan Satumba, shirin MANSOOR ya lashe
kyautar shiri mafi kayatarwa.

Shirin ta lashe kyautar sabanin sauran fina-finai
da aka hada su takarar na daga cikin fitattun
shirye-shirye na rukunin hausa.

A jawabin sa yayin da ya amshi kyautar Ali
Nuhu ya mika godiyan sa jaruman mda
ma'aikatan da suka taka rawar ganin wajen
shirya shirin MANSOOR.

Post a Comment

0 Comments