'Yan Sanda sun cafke wasu bayan sun yada sakonnin karya a WhatsApp -

Sakamakon yada labaran karya game da
wata matar aure da aka ce tana safaran
kananan yara, yan sanda a jihar Kano sun
kama shugaba da mambobin wani kungiyar
sadarwa ta Whatsapp.

Magaji Musa Maaji, kakakin rundunar
yan sandan Kano, ya bayyana cewa an
kama masu laifin ne bayan wata mata
ta kai korafi hukumar yan sandan

A cewar Magaji: “Mun samu korafi daga
wata matar aure da wani ma’aikacin
gwamnati, Misis Bushirat Madakim,
cewa ana yada hoton ta a wani shafin
WhatsApp inda ake yi mata kazafi.

WhatsApp ya ja an yi ram wasu Bayin Allah a
Kano
"Da muka ji korafinta, kwamishinan yan
sandan, Alhaji Rabiu Yusuf, ya bukaci ayi
binciken gaggawa, inda ana suka bi har
suka kama mutane uku masu aure,
namiji guda da mata biyu, kan laifin
yada bayanan karya.

“Da aka tunkare su akan tuhumar da
ake yi masu, masu laifin sun yarda cewa
hoton matar a shafinsu.

“Sun jadadda cewa basu taba ganin
matar ko zantawa da ita ba kafin su
fara yada labarin, inda suka bukaci a
yafe masu."

A yanzu dai an bayar da belin mutanen
yayinda ake ci gaba da bincike akan
lamarin.

Sannan yan sanda na ba matar
kariya saboda hotonta da yayi yawo da
gudun kada fusatattu su far mata.

Post a Comment

0 Comments