Fitaccen jarumin Kannywood, Adam A Zango
ya bayyana cewa sarki kwaya daya tal ne
kawai a masana’antar Kanyywood da ke
shirya fina-finan Hausa.
Adam Zango ya bayyana hakan ne a
shafukansa na kafofin sadarwa na zamani,
inda ya nuna cewa har yanzu Ali Nuhu ne
sarki.
Daga baya kuma sai ya saka wani hoto, inda
yake zugunne a gaban Ali Nuhu, shi kuma Ali
yana zaune a kan kujera, sai ya rubuta cewa
‘tuba nake sarki’.
Wannan lamarin ya zo ne a daidai lokacin da
wasu suke ganin akwai takun saka tsakanin
Adam Zango da Ali Nuhu, wanda har ake
tunanin yadda za a samar da zaman lafiya
na dindindin a tsakaninsu.
0 Comments