Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa
kuma daya daga cikin masu neman
jam’iyyar PDP ta tsayar da su takarar
shugaban kasa, ya ce Najeriya na cikin
mawuyacin halin rashin lafiya da take
bukatar ‘yan kasa nagari su gaggauta ceto
rayuwarta.
Lamido na wannan kalami ne yau,
Litinin, a Abuja, ga manema labarai
bayan kamala ganawa da wakilan
kungiyoyin kudu da tsakiyar Najeriya.
Kazalika, tsohon gwamnan ya bukaci
‘yan majalisar tarayya da su tsige
Buhari saboda laifukan yiwa kundin
tsarin mulkin kasa karan tsaye.
“ Duk abinda ke faruwa yanzu, na faruwa
ne saboda Najeriya bat a da lafiya.
Najeriya na bukatar shugaba da zai tafi
da duk ‘yan kasa ba tare da nuna
kabilanci ko bangaranci ba ,” a kalaman
Lamido.
Sule Lamido da Buhari
Sannan ya kara da cewa, “ tafiyar da
harkokin gwamnati na fuskantar
barazanar lalacewa a karkashin wannan
gwamnati, shi yasa ake ta aiiyukan
ta’addanci da kashe-kashe a Taraba,
Adamawa, Zamfara da ragowar sassan
Najeriya."
Kazalika, Lamidon ya zargi Buhari da
yunkurin binne irin gudunmawar da
mazan jiya suka bayar wajen gina
Najeriya, mutanen da ya ce Buhari ko
kafar su bai kama ba idan ana maganar
gaskiya da rikon amana.
“ Tun kafin zuwan Buhari akwai mutane
masu kima da gaskiya, akwai Tafawa
Balewa, Obafemi Awolowo, Aminu Kano,
da Azikiwe, wadannan mutane babu
wanda ke tantama a kan rikon amanrsu
da dattako. Ko sau daya Buhari bai taba
yabawa gudunmawar su ba ,” a cewar
Lamido
0 Comments