Siyasar Kano: Labarin rayuwar
siyasar Dr. Nasiru Yusuf Gawuna
Ana sa rai kwanan nan Majalisar dokokin
Jihar Kano ta tabbatar da Dr. Nasir Yusuf
Gawuna a matsayin Mataimakin Gwamnan
Jihar Kano.Yanzu dai mun ji cewa har an
aika sunan sa zuwa Majalisar Jihar.
Don haka ne mu ka kawo abubuwan da
ya kamata ku sani game da wanda ake
sa rai ya zama Mataimakin Gwamna
Abdullahi Umar Ganduje a Kano wanda
rikakken ‘Dan siyasa ne kuma
kasurgumin Attajiri.
Siyasar Kano: Labarin rayuwar siyasar Dr. Nasiru
Yusuf Gawuna
Nasiru Gawuna ya zama babban 'Dan
adawar Kwankwaso daga baya inda
kuma zai dare kan kujerar Mataimakin
Gwamna bayan Farfesa Hafiz Abubakar
wanda ke tare da Sanata Kwankwaso ya
bar kujerar.
1. Shugaban Karamar Hukuma
Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya rike
Shugaban Karamar Hukumar Nasarawa
a lokacin Malam Ibrahim Shekarau
yana Gwamnan Kano.
A lokacin mutane
sun tabbatar da cewa Gawuna yayi aiki
a Nasarawa.
2. Kwamishina a lokacin Kwankwaso
A lokacin Gwamna Rabiu Kwankwaso ne
aka nada Nasiru Gawuna a matsayin
Kwamishi a Jihar Kano.
Gawuna yana
da mutane da-dama musamman a
Yankin sa na Nasarawa a cikin Birnin
Kano.
3. Kwamishina a lokacin Ganduje
Nasiru Gawuna yana cikin wadanda
Ganduje ya tafi da su a mulkin sa ya
kara nada sa Kwamishinan noma.
Gwamna Abdullahi Ganduje ne yayi wa
Kwankwaso Mataimaki a lokacin yana
mulki.
4. Neman kujerar Sanatan Kano
Kafin yanzu dai Kwamishinan ya fara
hangen doke Sanata Kano ta tsakia
Rabiu Kwankwaso. Gawuna ya shirya
takarar Sanata a APC kafin tsohon
Gwamna Ibrahim Shekarau ya dawo
jam’iyyar.
5. Shugaban Kungiyar YFSN
Dr. Gawuna ya taba rike shugabancin
Kungiyar YSFN watau “Youth Sports
Federation of Nigeria” ta Matasan ‘Yan
wasan da ke Najeriya.
Gawuna mutum
ne mai matukar son kwallon kafa.
Kwanaki kun ji Rabiu Musa Kwankwaso
ya kai wa Janar Ibrahim Babangida
ziyara a gida. ‘Dan takarar Shugaban
kasan na PDP yayi kus-kus da IBB ne
inda ya nemi albarka a zabe mai zuwa
na 2019.
0 Comments