Assalamu alaikum yan uwa
iRashyder
LET'S TALK ABOUT MAKEUP
EPISODE : 10
Assalamu alaikum wa rahmatullah. Last week
mun fara magana akan concealer yanda zaki
saya da kuma wanda zai dace dake So, insha
Allah Yau zan gabatar maku da hanyoyi daban
daban wanda zaki iya amfani da concealer dinki
amma kafin nan akwai buqatar in qara tunasar da
mu wannan
YELLOW CONCEALER :- tana fitar maki da even
tone ma'ana zata sa kalar fatar ki ta fito sosai
PINK AND PEACH CONCEALER
Wannan kalar sun fi kyau a shafa su a under eye
wato ina nufin concealer da ake shafawa a qasan
ido
GREEN CONCEALER
wannan kalolin concealer din suna boye
blemishes wasu en chaki chaki pimples, tabo da
duk wasu dabbare dabbaren da suke a fuskar
mutum
ORANGE CONCEALER
Wannan especially mata masu amfani da niqaf
zaki ga zagayen idon su tayi baqi sabda rana tou
idan idonki yana da wannan duhun akwai buqatar
ki yi amfani da orange concealer a idon ki
PURPLE CONCEALER
swannan yana boye chaki chakin fuska
Wannan sune kaloli na concealer da ya kamata ki
mallaka alhmdl ynxn zaki iya samun su cikin arha
da sauki domin anyi su kamar eye shadow idan
kin je siya kawai kice a baki CONCEALER
PLATELET .
YANDA AKE AMFANI DA CONCEALER
Concealer tana da amfani a. Wurare iri daban
daban misali
1 MACE MARAR TABO
Ba dole sai kina da tabo a jiki zakiyi using
concealer ba a'a zaki iya amfani dashi wurin fitar
da asali shape din fuskar da Allah yayi maki
yanda zakiyi shine ki samu concealer kala biyu
mai haske da mai duhu (kamar yanda nayi
Bayani a post dina na last week idan baki gani
ba ki duba a Facebook page mai suna ADO DA
KWALLIYA ) ki shafa mai hasken a T zone dinki
da kumatun Ki mai duhun kuma ki shafa a
sauran sassan fuskar ki zuwa wuya sannan kiyi
Blending ki shafa powder.
2 MACE MAI TABO KO PIMPLES
ke kika fi chanchanta wurin amfani da concealer
sai ki sayi concealer na boye tabo ki shafa a kan
tabon kadai a duk fuskar ki ba fa! ki bari ya dan
sha iska kamar 5mins sannan sai ki dauko asalin
concealer din ki kalar skin naki ki shafa akan
green concealer din sannan ki shafa powder.
Idan baki da concealer zaki iya amfani da
foundation amma idan ki shafa sai kin jira
30mins ya yi kauri sannan ki shafa powder akai
PIMPLES A BAYA KO QIRJI
idan kina da pimples ko tabbai da yawa ko kadan
a jikin ki kuma kina sou ki sa kayan da dole sai
sun fito.....
Ki dauki normal concealer dinki kalar jikin ki sak!
Ki shafa a wurin amma fa tabon da pimples din
kadai zaki riqa rufe wa ba wai duk wajen zaki
yiwa fenti ba. Idan kin gama sai ki yi amfani da
brush ko soson pauda ki shafa pouda mai gari a
wajen sama sama ake shafawa ba da qarfi ba .
MARAR SON KWALLIYA / STUDENTS
Man shafawar ki ta fuska zaki dangwali kadan ki
shafa a bayan hannun ki hada da concealer da
foundation ki kwaba ki shafa a fuskar ki at once
ki shafa powder amma fa kadan kadan kar ki
cika idan kikayi haka kin hada TINTED
MOISTURIZER kenan amma baza ki iya hadawa
da yawa ki ajiye ba.
CONCEALER A QASAN IDO
- Hanya Mafi dacewa idan zaki shafa concealer a
kasan idon ki shine kiyi shape din triangle dashi
kamar yanda zaku gani a hoton .
- Sannan kar ki manta idan idonki yana da duhu
tou ki riqa amfani da orange, pink ko kuma
peach colour concealer a qasan idon sannan sai
ki rufe shi sama sama da asalin concealer dinki.
- akwai wasu layi layi a qasan idon ki idan kin
gama shafa concealer kinga sun fito sai ki nema
tissue ki rage wa tissue din kauri wajen cire palle
daya a jiki ki sa a qasan idonki zai tsantsame
maiko din.
CONCEALER A GIRA
-zakiyi amfani da concealer brush wurin fitar da
shape din girar ki ta sama da ta qasa sannan kiyi
amfani da yatsar ki ta zobe ki rage wa concealer
din karfi sosai kar ki bari ta fito dau
CONCEALER A IDO
- idan baki da eyeshadow primer zaki iya amfani
da concealer wato zaki dangwali concealer dan
kadan sai ki shafa a saman idonki amma fa kar
bari ya shiga ramin kashin idonki tou bayan kin
shafa sai ko shafa farin eyeshadow akai sannan
ki shafa duk kalar da kike sou hakan zai sa
eyeshadow din yayi kauri kuma ya tsaya a wuri
daya ba tare da wani layi layi ba.
-idan kina shafa eyeliner a ido kika yi mistake kar
ki damu idan kin gama ki sa abun share kunne ki
goge inda aka samu matsalar na San bazai fita
duka ba sai ki shafa concealer a wurin.
-ki fitar da shape din idonki ta hanyar shafa
concealer a saman kwayan idonki sannan ki
tsallake ramin qashin idanki ki shafa a qashin
girar da saqon idonki da ta qasan amma fa ba
yanda za'a gane ba yin hakan na da kyau
musamman lokacin da kika tashi daga barci
idonki luhu luhu.
CONCEALER A BAKI
-idan zaki shafa jambaki mai kala biyu bakya sou
su gauraya su zama daya zua anjima toh ki
shafa concealer a zagayen bakin naki inda zaki
amma banda tsakiya sai ki dan yi blending dinsa.
-idan kuma kina sou bakin ki yayi kauri kamar
mai shirin yin kiss tou zaki yi amfani da
concealer wurin fitar da shape din kiss a tsakiyar
bakin ki sai kiyi Blending sannan ki shafa jambaki
a hankali
-amma idan kina sou ki fitar da shape din bakin
ki ne tou wannan zaki shafa concealer a gaba
daya labban ki sannan ki shafa jambaki idan kin
gama sai kiyi amfani da concealer brush wurin
qara fitar da shape din bakin naki ta inda jambaki
ya bata.
CONCEALER A QASHIN WUYA
yanda zaki fitar da sexy night time look da
qashin wuyan ki shine ki samu concealer kala
biyu mai haske da mai duhu sai ki daga kafadun
ki sama ki shafa mai duhun a aljuhun da sukayi
mai hasken kuma a qashin saman sai kiyi
Blending dinsu yanda ba za'a gani ba.
Wannan sune da yawa daga cikin abubuwan da
nasan anayi da concealer don haka nike ganin
Gaskia ya kamata ki mallaki concealer kala kala
iri iri daban daban amma dai ki tabbatar kin fara
shafa foundation kafin concealer ba wai shafa
concealer a kasan foundation bashi da kyau bane
a'a sai dai yana buqatar kwarewa. dan Allah duk
wacce ta ji dadin abun da na rubta ta taya ni
addu'a bukatun mu na alkhairi Allah ya biya
mana Amin
Wslm
AdoDaKwalliya
0 Comments