iRashyder
LET'S TALK ABOUT MAKEUP
EPISODE 3 :
Jiya munyi magana akan dry skin Da effects
dinsa da kuma irin yanda zamu
Magance sa. Sai dai bamu fadi abubua
Da ya kamata mai dry skin ya riqa ci ba
Tou gaskia ya kamata mai dry skin ya riqa
Yawan cin fatty acid kamar Omega-3 da
Omega-6 daga nau'in abinci daban daban
Kamar su kifi, man waken suya, gyada,
da aleho (spinach ) da sauran su wannan
Kenan a yayin da mai oily skin ya kamata
Ya rage cin abubua da suka gaji maiqo.
DEHYDRATED SKIN
Wannan is somewhat type of dry skin Sai dai
shi xai iya Kasancewa a ko wane irin skin type
domin shi yana faruwa ne saboda illar karan cin
rua a jikin dan adam wanda idan hakan ya
kasance
Tou akwai matsala alamomin sa sune
Bushe wan wani bangare na jiki kamar fuska,
kalan fitsarin ki zai chanza zua orange maimakon
yellow, ko kuma kiji fatar ki tayi taurin,
Yawan ciwon kai da sauran su
REMEDY
Wannan ba skin type bane ke kika gayyato sa
Don haka maganin sa mai sauqi ne matuqar zaki
Kiyaye domin idan baki kula ba zai ja maki
manyan
Cututtuka abinda zaki yi mai sauki ne
1) yawaita shan ruwa kofi 6 ko 8 a rana ( ba dole
sai ruwa zallan zai cika kofi 6 ko 8 din ba kamar
tea, coffee, kunu da sauransu )
2) ki daina yawan amfani da beauty products
(Kayan shafa wanda basu karbi fatar ki ba)
3) ki riqa yawan Shan fruits
COMBINATION SKIN TYPE
Yanda zaki gane kina da skin combination shine
your T zone wato tsakanin goshi, ido, hanci, baki
da gemun ki suna da maiqo especially idan kikayi
kwalliya amma kumatun
Ki da sauran jikin ki basu da matsala tou wannan
combination skin gare ki
REMEDY
1) ki sai madara (kar kiyi amfani da skimmed
milk ko semi skimmed milk ) ki sa a wuta yayi
tausa ki ajiye a gefe ya huce idan yayi sanyi zaki
ga kamar leda a saman sa sai ki sa chokali ki
yade shi ki sa a wani kwano
2)ayaba guda daya ki raba shi uku ki dauki daya
ki nuqa yayi laushi sai ki fasa masa kwai daya da
zuma rabin chokali ki
3)sannan ki dakko wannan man da kika yade ki
hada a cikin hadin ayaban ki dama shi da kyau
ya hade sannan ki shafa a fuskar ki idan ya
Bushe ki dauraye da ruwa mai sanyi kar ki goge
fuskar ki barshi ya Bushe a haka
ki fasa kwai ki Cire na cikin ki bar farin ruwan
sai kiyi ta kada wa har sai yayi kumfa yayi kauri
kamar zakiyi cake sai ki barshi Ki zuba yoghurt
chokali daya ki kwaba ki sha a fuskar ki for
15-20mins sai ki wanke da ruwan dumi .
Ki samu rose flower guda daya sai ki tsinke
petals din shi guda 6 kiyi squashing dinsa cikin
rose water chokali daya ki sa zuma rabin chokali
da yoghurt rabin chokali juya yayi laushi ki shafa
a fuskar ki for 6-10 mins ki dauraye da ruwan
dumi
Finally ki riqa siyan face lotion daban (man
shafawa na fuska kadai ) wanda aka rubta for
COMBINATION SKIN thanks sai mun hadu A
NEXT EPISODE insha Allah
WomenOfJannah
0 Comments